✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin abinci mai gina jiki na hallaka yara a Nijar’

Kungiyar agaji ta Doctors without Borders ta yi gargadi kan karuwar mutuwar yara a Kudancin Nijar inda yara goma suke mutuwa duk rana a cikin…

Kungiyar agaji ta Doctors without Borders ta yi gargadi kan karuwar mutuwar yara a Kudancin Nijar inda yara goma suke mutuwa duk rana a cikin watan da ya wuce.

kungiyar ta ce mafi yawan mace-macen na da nasaba da karuwar yaduwar cutar maleriya da rashin abinci mai gina jiki wanda ya sa asibitocin yara da ke garin Magarya suka cika makil.

“Ba mu taba ganin irin wannan lamari ba, kuma muna tsoron cewa wannan somin-tabi ne” inji Dorian Job shugabar kungiyar a Nijar.

kungiyar ta ce cutar maleriya na karuwa duk shekara a irin wannan lokacin saboda yanayi, amma alkaluman bana sun bayar da mamaki.

Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyar na tunanin kashi daya cikin shida ne kawai na yaran da ke bukatar kula suka gani.

Dama can kungiyar MSF na tallafa wa al’ummar Magarya amma ta tura karin ma’aikatan jinya 243 bayan karuwar mace-macen, don kafa asibitocin tafi-da- gidanka domin duba yaran da ke bukatar kulawa.

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya da aka fitar a watan Afrilun bana sun nuna cewa an samu cututtuka miliyan 216 a shekarar 2016, wato an samu karuwa cututtuka miliyan 5 fiye da na shekarar 2015 a fadin duniya.

Kusan kashi 90 cikin 100 na mace-mace 445,000 da suka danganci maleriya a shekarar 2016 sun faru ne a Afirka.

Kashi 70 na mace-macen sun faru ne tsakanin yara ’yan kasa da shekara biyar, kamar yadda BBC ya rairayo.