✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin iya aiki ke sa a kosa da kallon fim –Yusuf Magarya

Kwanan baya Kungiyar Matasan Arewa ta Najeriya ta karrama fitaccen mai shirya fina-finai kuma Shugaban Kamfanin Magarya Film Production da ke Kano,Yusuf Muhammad Magarya. Wakilinmu …

Kwanan baya Kungiyar Matasan Arewa ta Najeriya ta karrama fitaccen mai shirya fina-finai kuma Shugaban Kamfanin Magarya Film Production da ke Kano,Yusuf Muhammad Magarya. Wakilinmu  ya tattauna da shi, inda ya bayyana cewa rashin iya rubuta labarin fim kan sa ya ginshi mai kallo.

 

Wadansu maso kallon fim suna nuna rashin jin dadinsu kan yadda fim ke ginsarsu kafin a gama, ko me ya sa?

Ba zan ce maka ba a samun irin wannan matsalar ba, amma ba a kowane fim ba. Duk dan Adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba. Wani lokaci duk yadda ka yi kokarinka sai an samu wani wajen da ajizanci ya dan taba mutum. Sannan abu na biyu shi ne duk fim din da ka ga labarin bai yi maka ba, ka tsaya ka duba ka ga wane kamfani ne ya yi fim din. Ka san akwai masu yin fim akwai kuma muna fim. Yanzu a ce ka kalli fina-finan Kamfanin UK Entertainment, ko na Maishadda Inbestment, ko FKD da irin su Sheshe Mobies ko ka kalli na Magarya Productions ai ka san fina-finansu sun tsere tsara. Na tabbata idan ka kalli fina-finan kamfanonin da na zayyana maka ba za ka ji cewa sun ginshe ka ba, ballantana ka cire. Na san ba za ka iya kyalewa nuni daya ko biyu ya wuce ka ba sai ka kalla har karshe. Ka san a kowace harka akwai ’yan koyo, to ta iya yiwuwa idan Allah Ya hada ka da na ’yan koyo aka yi dace sabon mai shirya fim ne ko sabon darakta ne yana kokari ya koyi sana’ar ce, to a irin wadancan fina-finai ne za a iya samun irin wadannan matsaloli. Haka ma wanda ya rubuta labarin abin lura ne. Idan ka hadu da irin wadannan kamfanoni dole ka ji fim din ma ya fita maka daga rai ka cire shi.

Yaya ake bi wajen karrama jarumai da kuma fina-fina?

Batun bayar da kyaututtuka akwai hanyoyi da yawa da ake bi ko ake dubawa. Na farko duk wanda ka gani an ba shi kyauta gaskiya sai an zauna an duba fim dinsa kuma sai ya cike takardar shiga gasar domin neman ya samu kyautar. Saboda akwai kamfanoni da jarumai da sauran hanyoyi da ake bi ake dubawa kafin a tantace a ba wanda ya yi nasara kyautar.

Misali ina godiya ga Allah, kamar wata daya da ya wuce na samu kyauta. Wani za ka ga an bi mataki a bangaren wanda ya fi kowa iya yi wa ’yan wasa kwalliya, wani kuma a bangaren darakta wasu kuma ta bangaren jarumi mai tasowa, ko kuma wanda ya fi kwarewa a iya siddabaru  ko babban jarumi ko jaruma, wani lokaci ana bin kamfanin da ya fi kowanne iya shirya fim. Su masu tantancewa su ne za su tsaya su kalla sannan su duba su ga wanda ya fi dacewa da kyautar, sannan a ba shi.

Yaya aka yi Matasan Arewa suka karrama ka?

Ina gode wa Allah bisa kyauta da kungiyar matasan Najeriya wadda ake kira da Arewa Kutashi Award, dama ita kungiya ce wadda take shirya kyaututtuka irin wadannan domin zaburar da samari su rike sana’a ba tare da sun dogara da aikin gwamnati ba. To wannan kungiya ta karrama ni a matsayin shugaban kamfanin da ya fi kowane kamfani a wannan shekarar iya shirya fim, amma hakan ba yana nufin ni na fi sauran ba ne ko kuma su ba su iya ba, na  shiga takarar ce da wani fim mai suna Madubin Dubarudu.

Yadda aka tantance kuwa shi ne; su masu shirya wannan gasa sukan dauki fina-finai kwarara kamar uku zuwa hudu kuma kamar mutum goma ko fiye da haka za su duba yadda ka dauki fim din, sannan akwai masu duba yadda ka sa fitila , wanda ke duba murya daban. Wadannan mutane idan sun zauna sun tantance su ne suke fitar da wanda ya fi a kowane daga cikin fina-finan da suka tantance. To wannan fim din da na fada maka Madubin Dubarudu shi ne aka zaba matsayin wanda ya fi, sannan aka ba ni kyauta.

Wane tanadi ake yi wa rayuwa ganin cewa wadansu da suka jima suna harkar fim sukan kare ba su da muhalli ko jarin da za su rike rayuwarsu?

Tanadi dai insha Allahu bai wuce daya ko biyu ba, wato gaskiya da rikon amana. Duk wanda yake rike da jari yana kuma taimaka wa ’yan uwa, to babu laifi.

Wane sako kake da shi ga masu bibiyar  fina-finan kamfaninka?

Sakona gare su na farko ina alfahari da su kuma lambobin da muka sanya a jikin fastocin fim ko a cikinsa muna bayarwa ne domin inda aka ga gyara a kira mu a yi mana bayani, kuma za mu gyara. Kuma koyaushe kofa a bude take na karbar gyara da shawarwarinku tunda dama domin bukatarku ce muke yin harkar.