✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin jari ne ke hana mu ci gaba – Masu yin takalma a kofar Wambai

Masa sana’ar yin takalma a kofar Wambai sun bayyana rashin karfin  jari a matsayin abin da ke zama kalubale ga sana’arsu wanda har ya sa…

Masa sana’ar yin takalma a kofar Wambai sun bayyana rashin karfin  jari a matsayin abin da ke zama kalubale ga sana’arsu wanda har ya sa ba su iya samar da takalma wadanda ke daidia da zamani.

Malam dahiru Abdulahi Mataimakin Shugaban kungiyar ya bayyana wa Aminiya cewa babu shakka da za a samu gwamnati da za ta shigo ciki a basu jari, da za su iya zarce takwarorinsu da ke garin Aba ta Jihar Abiya. “Babu shakka mun fi su iya yin takalma masu ingaci. Abu biyu suka fi mu wato karfin jari da kuma hadin kai. ’Yan Aba suna da kudi sosai a hannunsu haka kuma gwamnatinsu na taimaka musu. Mu masu yin takalma a nan marasa jarin sun fi masu jarin yawa. Sannan kuma abu na biyu anan ba mu da hadin kai, a yanzu idan na ga wani ya kera takalmi ya yi min kyau, to sai na je na yi irinsa ba tare da nema izininsa ko wani abu ba. A Aba kuwa ba haka ake yi ba, komai ana yinsa ne bisa doka. Idan ka ga wani takalmi za ka yi irinsa to dole saa ka nemi izinin wanda ya yi shi, idan kuma mutum bai yi hakan ba to kungiya za ta iya ladabtar da shi.”

Mataimakin Shugaban ya dora alhakin rashin samun ingancin takalman da suke yi akan  masu sayen takalma daga hannunsu inda suke nuna sun fi son a yi musu takalma masu arha. “ba wai nufinmu mu rika yin takalma marasa inganci ba, a’a, abokan cinikinmu ne ke sa mu mu yi musu dai dai da kudin da za su iya saye. Idan ma mutum ya je ya yi takalmi mai kyau to ba za a saya a farashinsa ba. Saboda akwai mutanenmu da za su iya yin irin wannan takalmin ta hanyar yin amfani da kayayyaki marasa inganci wato wadanda ke da saukin kudi, don haka idan suka tashi sayarwa dole a sayar da su da arha.”

Ya bayyana cewa duk da cewa sukan kwaikwayi kirar takalman kasashen waje, sun fi yin takalma bisa kirkirarsu. “ A gaskiya mun fi yin takalmanmu bisa kirkira. Muna fitar da takalma iri-iri. Idan muka samo wata kirar sai mu nuna wa abokan sana’armu. A nan kuma za a ba mu shawarar yadda za a gyara.  A wasu lokutan kuma muna kwaikwayon takalaman kasashen da yawa ‘yan waje suna shigowa cikin kasuwarmu su dauki takalmanmu su tafi da shi a yi musu a can. Domin akwai lokacin da wasu yan China suka zo suka karbi takalmanmu daga baya suka rika yin kwatankwacinsu suna kawo wa ana sayarwa a cikin kasuwa.

Hakanan kuma ya bayyana cewa baya ga ire-iren takalman da suke yi a radin kansu, har ila yau sukan yi takalman irin wanda mai saye yake so a masa “mukan yi takalma don masu sari su saya su kasa a shaguna ko kuma masu zuwa daga wurare daban daban da suka hada da Maiduguri da Sakkwato da sauransu da suke zuwa suke sayen takalmanmu, a gefe daya kuma muna yin takalma bisa tsarin da mai saye yake so, ma’ana yanayin zabinsa.”

Sannan kuma mataimakin shugaban ya yi kira ga gwamnati da ta kara bunkasa makaratar nan ta koyan aikin takalmi wacce gwamnatin baya ta yi don masu sana’ar su kara samun gogewa.  “Akwai wata makaranta ta koyon aikin takalma da Gwamna Kwankwaso ya yi a rukunin masana’antu na Sharada don haka muke so a bunkasa wannan makaranta yadda za mu kara Gogewa. Kin san yanzu akwai abubuwa na zamani da suke shigowa don haka ba mu so a bar mu a baya.”

Har ila yau mataimakin shugaban ‘yan takalman ya bayyana cewa karin kudaden rumfuna da aka yi a cikin kasuwar ta kofar Wambai ya kori da yawa daga cikin masu sana’ar takalman daga cikin kasuwar. “sai ki ga mai yin takalmi ya dade a shago bayan ya raya wurin. A matsayinsa na mai karamin karfi yana biyan Naira dubu 20, sai ki ga wani babban dan kasuwa ya zo ya nuna yana son shagon, a kudi mai yawa, don haka sai a karshe a kori mai sana’ar takalmi.

‘Yan takalman sun nemi gwamnati ta yi doka wajen tsayar da farashin kayayyakin aikin takalmi, kasancewar tsadar kayayyakin ma na zama barazana ga sana’ar tasu.