Da Dumi Dumi

Rashin kudi da makamai ya haddasa kawar da Boko Haram– Ahmed

Mahalarta taron da aka yi a Maiduguri

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmad Lawan ya ce sai gwamanati ta ware isassun kudi da makamai sannan za’a iya kawo karshen yaki da Kungiyar Boko Haram.

Ya ce, jami’an tsaro suna sane da wasu wurare uku da har yanzu ake fama da matsalar ta Boko Haram a jihar Borno, sai dai rashin isassun kayan aiki ne yake hana su yin nasara a kan ‘yan Boko Haram din.

Sanata Ahmad Lawan, wanda Sanata Ali Ndume ya wakilta, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayani a taron samar da tsaro na yankin Arewa maso Gabas, wanda ofishin babban Sufetan ‘yan sanda na kasa ya shirya a garin Maiduguri.

Taron wanda ya gudana karkashin jagorancin Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya samu halartar shugaban Rundunar ‘yan sanda ta kasa, Mohammed Abubakar Adamu, da Gwamnonin jihohin da suka hada da: Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe‎. Sai ‘yan majalisun tarayya, jami’an tsaro, Sarakunan Gargajiya da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

Ahmad Lawan ya kara da cewa, matukar ana son a kawo karshen yakin Boko Haram to ya zama dole a samar da kayayyakin aiki na zamani da jami’an tsaro zasu yi aiki da su.

ADVERTISEMENT

“Mafiya yawan mu anan duk ‘yan gudun hijira ne, an raba mu da garuruwanmu da dukiyoyin mu saboda wannan yaki na Boko Haram. Sai dai muna fatan wannan taro ba zai tsaya iya nan ba. Muna fatan za’a aiwatar da dukkanin abubuwan da aka tattauna”, in ji Ahmad Lawan.

A karshe ya bayyana cewar, jami’an tsaron kasar nan sun yi kadan domin kuwa sojoji dubu 154 da ‘yan sanda dubu 400 sun yi kadan wajen bada tsaro a Najeriya.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya