Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Rashin makarantar Islamiyya ne babban kalubalen Musulmin Ubolafor

Rashin makarantar Islamiyya ne babban kalubalen Musulmin Ubolafor

Babban Limamin Masallacin Juma’a da ke Ubolafor a Jihar Enugu, Sheikh Isma’il Ngwo ya ce, babban kalubalen da Musulmin garin ke fuskanta shi ne na rashin makarantar Islamiyya da za su rika karantar da yara addinin Musulunci.

Sheikh Ngwo, ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilin Aminiya, inda ya ce halin yanzu “Masallacin ba ya da makarantar Islamiyya. Na yi magana har yanzu ba a samu wanda zai gina mana makarantar Islamiyya ba,” inji shi.

A cewar limamin, masallacin zai iya daukar masallata sama da dubu biyu.

Ya ce, wadansu bayin Allah ne suka dauki dawainiyar gina masallacin.

Wani da ake kira Alhaji Waziri, shi ne ya gina masallacin. Ya ce masallacin na Ubolafor an bude shi ne ranar Juma’ar da ta gabata 21 ga Fabrairun nan.

Limamin ya bukaci al’ummar Musulmi ’yan asalin yankin Kudu maso Gabas su fahimci cewa addinin Musulunci addini ne na zaman lafiya da kaunar juna kuma irin yadda kabilar yankin suke da yawan Musulmi su ci gaba da neman ilimin addini yadda za su bauta wa Mahaliccinsu.