✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin soyayya da ma’amalar iyali ta haifar da yawan sakin aure a Saudiyya

Rashin iya soyayya da mu’amalar tarawa da iyali ta haifar da sakin aure har dubu da 600, cikin watanni 15, a kasar Saudiyya; kuma an…

Rashin iya soyayya da mu’amalar tarawa da iyali ta haifar da sakin aure har dubu da 600, cikin watanni 15, a kasar Saudiyya; kuma an dora mafi yawan alhakin a kan mazaje, kamar yadda shafin yada labarai na Emirates 24/7 ya ruwaito.
Ma;aikatar Shari’a ta kasar, ta fitar da alkaluman rikice-rikicen aure da ke gaban kotu, wadanda yawansu ya kai dubu da 371, daukacinsu duk mata ne ke neman mazansu su sake su, bisa laifin rashin Tarawa da su.
Kotu ta yanke hukunci kan kararraki 283, wadanda mazajen suka kai, inda suka zargi matansa da kin Tarawa da su.
Jami’an Hukuma, sun bayyana cewa yawan alkaluman sakin auren da aka bayyana ya wuce yadda ake zato.
Wani farfesa da ke koyar da darussan addinin Musulunci a wata Kwalejin kere-kere da ke birnin Riyadh, ya bayyana cewa: “A kan samu kiyayya tsakanin ma’aurata. Don haka alkaluman da kotu da bayyana sun fi haka, tunda dimbin matsaloli tattare da aure.”
kasar Saudiyya mai yawan al’umma kimanin miliyan 30, ita ke da mafi yawan sakin aure a duniya. Sai kuma sauran kasashen da ke yankin Tekun Fasha da ke iye mata. kididdiga dai ta nuna a kowacce rabin sa’a ana sakin aure a kasar Saudiyya.
kasar Saudiyya da sauran kasashen Yankin Tekun Fasha sun yanke matsaya, wajen shirya bita ga masu shirin yin aure, tare da bai wa saurayi da budurwa damar ganawa da juna, ta yadda za su yanke wa kansu hukunci, kan ko sun cancanci zama mata da miji.