✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin Tsaro: Matasa sun yi bore a Katsina

Daruruwan matasa sun tare titin Kastina-Kankara don nuna bacin ransu kan matsalar rashin tsaro a jihar Katsina. Fusatattun matasan sun tare babban titin garin Yantumaki…

Daruruwan matasa sun tare titin Kastina-Kankara don nuna bacin ransu kan matsalar rashin tsaro a jihar Katsina.

Fusatattun matasan sun tare babban titin garin Yantumaki da ke Karamar Hukumar Danmusa, ga dukkan masu ababen hawa.

Boren na zuwa ne kwana guda bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani ma’aikacin lafiya da diyarsa a yankin.

Masu zanga-zangar sun ce kusan kullum sai ‘yan bindiga sun kai hari a garuruwansu, kuma babu alamar za a shawo kan matsalar.

Ko a makon jiya wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki Alhaji Atiku Maidabino a gidansa.

Matasan sun hana motoci bi ta hanyar domin nuna fushinsu kan yadda matsalar ‘yan bindiga ta ki ci ta ki cinyewa a yankin.

Tarzomar ta sa daruruwan masu ababen hawa kaurace wa hanyar da ta tashi daga Katsina ta isa zuwa Gusau a jihar Zamfara.