✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rashin wutar lantarki ya jefa kamfanoni da masana’antu a mawuyacin hali’

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhhuna ta Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin  Alheri Group da ke garin Jos, Alhaji Iliyasu Muhammad ya ce kamfanoni da…

Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Buhhuna ta Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin  Alheri Group da ke garin Jos, Alhaji Iliyasu Muhammad ya ce kamfanoni da masana’antun Najeriya, suna dada shiga cikin mawuyacin hali sakamakon rashin wutar lantarki, bayan da gwamnati ta sayar da kamfanin wutar lantarki ga ’yan kasuwa.

Alhaji Iliyasu Muhammad ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos, inda ya ce a zamanin gwamnatocin da suka gabata kafin wutar lantarki ta koma hanun ’yan kasuwa,  kamfanoni da masana’antun Najeriya  suna samun wutar lantarki na awa 8 a kowace rana.

Ya ce amma yanzu kamfanoni da masana’antu ba su da wani tsari na samun wutar lantarki a kasar nan, saboda wannan sabon tsari da aka koma na mika harkar ga ’yan kasuwa.

Ya ce “Tunda wutar lantarki   ta koma hannun ’yan kasuwa a Najeriya abubuwa suka dada lalacewa. Domin ’yan kasuwar  ba sa iya sayo yawan wutar lantarkin da za su raba wa al’ummar kasar nan. Yanzu kamfani ko masana’anta zai iya zuwa sayen wuta a ce ta kare, saboda wadannan ’yan kasuwa ba sa iya sayen wutar da zas u raba wa kowa da kowa.”

Alhaji Iliiyasu Muhammad ya ce matukar gwamnatin Najeriya tana son farfado da harkokin kamfanoni da masana’antu da kasuwanci a Najeriya, wajibi ne ta farfado da wutar lantarki a Najeriya. Kuma  ta rage kudaden harajin da take sanya wa ’yan kasuwa tare da  sassauta wa ’yan kasuwar farashin  canjin  Dala.