✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasuwar dalibai 20 a hadarin mota ta girgiza Jihar Bauchi

Garin Misau shi ne birni na uku mafi girma a Jihar Bauchi in aka cire garin Bauchi da Azare, kuma gari ne da al’ummarsa ke…

Garin Misau shi ne birni na uku mafi girma a Jihar Bauchi in aka cire garin Bauchi da Azare, kuma gari ne da al’ummarsa ke zaune lafiya.

Sai dai a yayin da mutanen garin suke ci gaba da gudanar da harkokinsu, kwatsam ranar Talatar da ta gabata sai ga labarin wani mummunan hadarin mota da ya girgiza daukacin mutanen garin da al’ummar Jihar Bauchi da kuma kasa baki daya. Ranar ta sauya tarihin zaman jama’a a Masarautar Misau inda jama’a suka shiga jimami da zaman makoki, sakamakon wannan mummunan hadari da ya yi sanadin rasuwar daliban Makarantar Sakandaren Jeka-Ka-Dawo ta Gwamnati da ke Misau su 20 da malamansu biyu.

Kusan ko’ina a garin ana zaman makoki ne a gidajen iyayen yara da na malamansu da hadarin ya rutsa da su.

Shugaban Makarantan Sakandaren Je-Ka-Ka-Dawo ta Gwamnati da ke Misau Malam Rabi’u Ahmed cikin jimami da kaduwa ya shaida wa manema labarai cewa, “daliban da malaman makarantar Allah ne ya kaddara cewa za su rasu a rana guda, kuma abin da Allah Ya kaddara babu makawa sai ya faru. Sun tashi daga Misau ne za su je Kano ziyara a Gidan dan-Hausa domin karin ilimi da ake kira (Edcursion), sai Allah Ya kaddari rasuwarsu baki daya a kan hanya kafin su isa cikin garin Gaya.”

Malam Rabi’u ya ce daliban suna cikin kulob din da ake ce kira Kulob din Hausa wata kungiya ta masu nazarin Hausa, amma a kan hanyarsu sai suka yi karo da wata babbar mota nan take Allah Ya karbi kwanansu.

Shugaban ya ce mutum 25 ne a cikin motar, 22 dalibai ne biyu kuma malamai, dayan kuma direba ne, kuma 23 Allah Ya yi musu rasuwa, dalibai 20 da malamai biyu da kuma direban motar.

Ya ce daga cikin wadanda suka rasu akwai mata 10, maza kuma 13, kuma daga cikin matan akwai malama daya mace, sannan dalibai mata tara, cikin maza kuma akwai malami daya namiji da direban motar da kuma dalibai maza 11.

Malam Rabi’u ya ce dukan wadanda suka rasu Musulmi ne shi ya sa aka yi musu jana’iza a fadar Mai martaba Sarkin Misau tare da shi Mai martabar. Ya ce sauran mutum biyu da ba su rasu ba an kai su Asibitin Kano amma yanzu an dawo da su asibitin Azare. “dazu ma mun tuntube su aka ce jikinsu da sauki suna kwance a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare.

Da yake bayyana halayen daliban da malaman da suka rasu, Shugaban Makarantar ya ce dalibai ne masu hazaka masu son neman ilimi haka su ma malaman mutane ne masu kaunar aikin koyar da dalibansu, kuma dukansu da daliban da malaman ba yanzu suka fara fita irin wannan neman karo ilimi ba. Ya ce sukan je su Bauchi da Sakkwato da sauransu kuma duk inda za su je tare da wadannan malamai suke zuwa. “A gaskiya na yi rashin malamai masu matukar kokari a harkar gudanar da makarantar nan,” inji shi.

daya daga cikn malaman makarantar, Malam Abubakar Ahmed wanda yake karantar da darussan pizik (Physics) da sinadarai (Chemistry), ya ce wannan abu Allah ne Ya kawo shi, ba yadda muka iya, Allah da ikonSa mutum 25 da suke cikin motar babbar mota ta bi ta kansu da mata da maza 23 sun rasu saura malami daya da dalibi daya suna jinya.

Malamin ya bayyana sunan malaman da suka rasu da Malam Muhammed Mohammed da Malama A’ishatu Jarma kuma ya nuna godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano da Shugaban karamar Hukumar Gaya da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano da Sanata Kabiru Gaya wadanda suka taimaka bayan abin ya faru aka kwashe daliban. “Kamar Shugaban karamar Hukumar Gaya, da shi aka yi musu Sallar Jana’iza a nan Misau,” inji shi.

dan sandan da ya rako gawarwakin daliban zuwa Misau, Sufeto Haruna Gaya ya ce daliban sun yi taho-mu-gama ne da babbar mota kirar tirela kuma nan take mutanen suka rasu.

Malam Nasiru Darazo wanda kanensa shakiki ke cikin daliban da suka rasu ya nuna alhininsa game da faruwar lamarin sai ya yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama.

Ya ce in ka ga gawarwakinsu abin ba kyan gani wani kansa ya karye wani hannuwa har kayan cikinsu wadansu ma ana gani. “Allah Ya sa mu cika da imani,” ya fada yana hawaye.

Nasiru Darazo ya ce an yi wa mamatan jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a fadar Sarkin Misau tare da Sarkin da dubban Musulmi da suka fito daga cikin garin Misau da kewaye. Babban Limamin Misau, Imam Usman Baba ne ya jagoranci Sallar Jana’izar.

Ya ce bayan da aka yi musu Sallah sai aka kai su makabarta inda gireda ta tona manyan ramuka biyu sai aka bi cikin kowani babban ramin aka yi wa kowani mutum kabarinsa daga bisani aka rufe su inda aka rufe maza 13 cikin rami daya mata goma kuma cikin babban rami guda.

Wata mahaifiya da muka nemi zantawa da ita kasa magana sai cewa take yi ’yata Na’ima ta rasu tana Babbar Sakandare aji uku.

Lokacin da ya kai gaisuwar ta’aziyya ga iyayen mamatan Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Muhammad Abdullahi Abubakar ya roki Allah Ya jikan mamatan kuma Ya sanya su cikin Aljanna musamman da yake sun rasu ne a kan hanyar neman ilimi.

Gwamna Abubakar ya ce Allah ne Ya yi umurni da a nemi ilimi maza da mata don haka wadanda suka rasu a hanyar neman ilimi ana yi musu fatar samun gafara a wajen Allah. Sai ya dauki nauyin jinyar sauran wadanda suke jinya kuma ya ba da tallafi ga iyalan wadanda aka yi wa rasuwar.

Mai martaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Suleiman ya gode wa Gwamnan saboda yadda ya katse ayyukan da yake yi ya kai gaisuwar ta’aziyyar sai ya roki Allah Ya jikan wadanda suka rasu shi kuma Ya ba shi lada.

Sarki Ahmed ya kuma ja hankalin iyaye cewa duk da faruwar wannan lamari su kula da karatun ’ya’yansu.

Da yake gabatar da ta’aziyyarsa Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya roki Allah Ya jikansu mamatan inda ya ce wannan babban rashi ne ba ga Masarautar Misau kawai ba har da Jihar Bauchi da Najeriya baki daya.

A ta’aziyyar Shugaban Majalisar Wakilai, Honorabul Yakubu Dogara ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu, inda Kakakinsa Turaki A. Hassan ya ruwaito shi yana cewa:  “Ina cike da kaduwa da bakin ciki, kan rasuwar wadannan yara. Sun rasu a lokacin da suke kokarin neman ilimi a kokarinsu na zama manyan gobe a kasar nan.”

“Wannan babban rashi ne ga kasa. Wadannan yara alamu ne na kyakkyawar fata da suka nuna himma ta samar da kyakkyawar al’umma, rasuwarsu kwatsam wata babbar asara ce ga Najeriya, domin Allah ne kawai Ya san abin da za su iya zama a nan gaba,” inji Dogara.

“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyayensu da dalibai da malaman Sakandaren Gwamnati ta Misau da Masarautar Misau da daukacin al’ummar Jihar Bauchi, kan wannan mummunan hadari. Babu wata kalma ta rarrashi da za a iya fada ta kau da alhini da jimamin da iyayen suke fama da su kuma rasuwar kananan yara irin wadannan da su ne shugabannin gobe babban rashi ne ga shi kuma a hanyar ilimi,” inji shi

dan Majalisar Wakilai daga Mazabar Misau da Dambam, Malam Ahmed Yerima ya yi adduar Allah Ya jikan mamamatan sannan ya ja hankalin iyaye cewa kada faruwar wannan lamari ya karya musu kwarin gwiwa wajen tura ’ya’yansu makaranta, kuma ya tallafa wa iyayen yaran da malaman da suka rasu.