✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasuwar mahaifiyar Sarkin Ilori ta girgiza Hausawa mazauna Kwara

A daren ranar Karamar Sallar da ta gabata ce Allah Ya yi wa mahaifiyar Mai martaba Sarkin Ilori da ke Jihar Kwara Alhaji Ibrahim Sulu…

A daren ranar Karamar Sallar da ta gabata ce Allah Ya yi wa mahaifiyar Mai martaba Sarkin Ilori da ke Jihar Kwara Alhaji Ibrahim Sulu Gambari rasuwa, aka kuma yi jana’izarta a ranar Sallah bayan an sauko daga Idi.

Hajiya A’isha Zulkannaini Gambari ta rasu tana da shekara 124, marigayiyar jika ce ga Sarkin Ilori na 7 sannan ’ya ce ga Sarkin Ilori na 8 kana mata ga Sarkin Ilori na 9, kuma ’yar uwa ce  ga Sarkin Ilori na 10 kuma mahafiyar Sarkin Ilorin na 11.                                                                                                                                                 Al’ummar Hausawa mazauna Jihar Kwara sun nuna alhininsu tare da jimamin rasuwar mahaifiyar Sarkin Ilorin wacce suka bayyana ta a matsayin uwa gare su da suke kai wa ziyara a duk lokacin da suke bukatar samun natsuwa.

Alhaji Usman Adamu Sarkin Fulanin Jihar Kwara ya shaida wa Aminiya cewa, duk da kasacewar mahaifiyar Sarkin Ilorin tana da yawan shekaru amma ba ta yi jinya ba domin tare da ita suka yi ta halartar wa’azuzzuka da sauran tafsiran watan Ramadan.

Mai martaba Sarkin Ilori Alhaji Ibrahim Sulu Gambari
Mai martaba Sarkin Ilori Alhaji Ibrahim Sulu Gambari

“Mun gode wa Allah ta cika a daren Sallah wannan ba karamin dace ba ne, Hajiya ta kasance mai son jama’a mai son baki ce, za mu iya cewa mu aka yi wa rashi, fatanmu Allah Ya jikanta Ya yi mata rahama, domin duk wanda ya yi  rayuwa irin nata a kan tafarkin Allah sai ya gode wa Allah,” inji shi.

Sarkin Hausawan Jihar Kwara Alhaji Abubakar Ibrhami, cewa ya yi marigayiyar dattijuwa ce mai rikon addini tare da son jama’a, “Tana da matukar riko da addini, a gaskiya mu ’yan Hausawa mazauna Jihar Kwara mun yi rashi, fatarmu Allah Ya jikanta Ya yi mata rahama, mu kuma in lokacinmu ya yi Ya sa mu dace mu cika da imani. Ina mika sakon ta’aziyyata a madadina da duk Bahaushe ko Bafulatani mazaunin Jihar Kwara,” inji shi.

Fadar Sarkin Ilorin da ke birnin wacce babbar kasuwar jihar ta yi wa kawanya tana ci gaba da karbar manyan baki da ke zuwa gaisuwar ta’aziyyarsu ga fadar bisa rasuwar mahaifiyar Sarki Alhaji Ibrahim Sulu Gambari.

Sarkin Hausawan Jihar Kwara Alhaji Abubakar Ibrahim
Sarkin Hausawan Jihar Kwara Alhaji Abubakar Ibrahim