‘Rasuwar matar Abubakar Tafawa Balewa babban rashi ne’

Marigayiya Hajiya A’ishatu Tafawa Balewa
Marigayiya Hajiya A’ishatu Tafawa Balewa

An bayyana rasuwar Hajiya A’ishatu Abubakar Tafawa Balewa matsar tsohon Firayi Minstan Najeriya Sa Abubakar Tafawa Balewa a matsayin babban rashi ga iyalanta da Jihar Bauci da Najeriya.

Iyalanta da jami’an gwamnatin jihar da na tarayya da sauran al’umma ne suka bayyana haka.

Marigayiya Hajiya wadda aka fi sani da Jummai ita ce matar marigayi Sa Abubakar Tafawa Balewa da ta rage daga cikin matansa hudu.

Ta rasu ne a ranar Lahadin da ta wuce a wani asibiti da ke Legas bayan ta yi fama da jinya.

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ne ya dauki nauyin kai ta wani asibiti a Indiya don a yi mata magani bayan ta samu sauki ne, ta dawo Najeriya.  A daidai lokacin da ta sauka a Legas  sai rashin lafiya ya sake kamata inda Allah Ya yi mata cikawa a ranar Lahadin da ta wuce.

ADVERTISEMENT

Rahotanni sun nuna jim kadan bayan ta rasu sai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Marshal Sadik Abubakar ya bayar da jirgin sama don kai gawarta  Bauchi inda aka yi mata Sallah a Fadar Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu.

Jikan marigayin, Alhaji Billy Adamu Tafawa Balewa ya ce ita kadai ta rage musu daga cikin matan kakansu Tafawa Balewa. Ya ce lallai sun yi rashi don ta kasance uwa kuma kaka a daukacin zuriyyarsu.

Babban Limamin Bauchi Alhaji Bala Ahmad ne ya jagoranci yi mata Sallah.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izarta akwai Gwamnan Jihar Bauchi Alhajii Bala Mohammed da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar  da sarakunan Bauchi da Katagum da Misau da Ningi da Dass da wakilan Sarkin Jama’are da sauran jama’a.

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya jagoranci ayarin Gwamnatin Tarayya a madadin Shugaban Kasa Buhari wajen yi wa iyalanta da al’ummar Jihar Bauchi ta’aziyya.

Hajiya A’ishatu ta rasu tana da shekara 85 kuma ta bar ’ya’ya da jikoki masu yawa.  Daga cikin ’ya’yanta akwai Hajiya Yalwa Abubakar Tafawa Balewa da ke aiki a ma’aikatar ciniki ta Jihar Bauchi.