✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Raul Albiol na shirin barin kulob din Madrid

dan kwallon baya a kulob din Real Madrid Raul Albiol ya fara shirin barin kulob din zuwa na Napoli da ke Italiya kamar yadda jaridun…

dan kwallon baya a kulob din Real Madrid Raul Albiol ya fara shirin barin kulob din zuwa na Napoli da ke Italiya kamar yadda jaridun da ke Sifen da kuma na Italiya suka ruwaito.
Rahotani sun tabbatar kulob din Napoli ya taya dan kwallon ne a kan Yuro miliyan 12 kuma ga dukkan alamu kungiyoyin kwallon kafar biyu sun cimma matsaya.
Raul Albiol, mai kimanin shekara 27 tun cikin shekarar 2009 ya koma Madrid daga balencia da ke Sifen.
Yana daga cikin ’yan kwallon Madrid da ba kasafai suke buga wasa ba don haka  ya yanke shawarar canza sheka.
Idan cinikin ya kaya, Raul Albiol zai zama dan kwallo na biyu da ya bar kulob din ba ya ga Jose Callejon.