✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rawar da sabbin gwamnnoni suka taka cikin shekara daya

Yawancin gwamnoni a Najeriya, musamman wadanda a karon farko suke cika shekara guda, sun yi wa masu kada kuri’a a jihohinsu alkawura daban-daban kafin su…

Yawancin gwamnoni a Najeriya, musamman wadanda a karon farko suke cika shekara guda, sun yi wa masu kada kuri’a a jihohinsu alkawura daban-daban kafin su samu hawa karaga mulki.

Bayan cika shekara daya da kaiwa ga madafun iko, masu kada kuri’a a yankuna daban-daban sun fara lissafa nasarori ko kuma akasin haka da sabbin gwamnonin suka yi game da cika alkawuran da suka dauka.

Tambayoyin da ke yawo a bakunan jama’a dai su ne shin ko gwamnonin sun kama hanyar cika alkawuran da suka dauka?

A wannan nazarin, za mu mayar da hankali a kan jihohi shida wadanda suka hada da Gombe, da Bauchi, da Nasarawa, da Kwara, da Legas da Oyo wanda dukka suke da sabbin gwamnoni.

Gombe

A Gombe, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya samu darewa kan karagar mulki ne yayinda al’ummar jihar suke tsammanin abubuwa da dama daga gare shi.

Bayan shan rantsuwar kama aiki, Gwamna Yahaya ya jaddada alkawuran da ya yi na magance matsalar karancin ruwan sha, durkushewar bangaren kiwon lafiya, farfado da harkar ilimi, samar da aikin yi da kuma inganta tsaro a fadin jihar.

Duk da cewa ya dauki tsawon watanni shida kafin ya nada kwamishinoni, majalisar da ya nada ta dauki aikin farfado da jihar da kuma inganta ababen more rayuwa wadanda suka hada da gina hanyoyi a birane da ma kauyuka ciki har da karasa wasu da gwamnatin da ta gabata ta faro.

Ya kuma kulla hadin gwiwa da hukumomin raya kasa wurin samar da cibiyar kiwon lafiya a kowace mazaba a jihar.

Hakan ya kuma hada da sake karfafa asibitin kwararru da kuma wasu makarantu a jihar.

Gwamnan ya kuma gabatar da kudurin kafa gandun daji a Dadin-Kowa da kuma makiyaya a yankin Wawa-Zange.

Bugu da kari, sabuwar gamnatin ta kaddamar da wani shiri na ganin an sanya yaran da ba sa zuwa makaranta a makarantu.

Gwamnatin ta jihar Gombe a karkashin Inuwa Yahaya ta kuma faro aikin dashen bishiyoyi miliyan hudu wanda za a yi a tsawon shekaru hudu a jihar.

Duk da nasarorin da ta samu, al’ummar jihar suna ci gaba da fama da karancin ruwan sha, hakan ya sa akasarin wadanda suke zaune a birnin Gombe suka dogara kacokan a kan masu sayar da ruwa.

Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa an samu koma baya a jihar saboda janye kudurin karin albashin ma’aikata saboda tasirin cutar coronavirus.

Haka kuma, bayan da aka rushe shuwagabannin kananan hukumomi 11 a jihar, har yanzu gwamnan bai nada wadansu sabbi ba sabanin yadda Kundin Tsarin Mulki ya zayyana.

Za dai a ci gaba da zuba wa Gwamna Yahaya ido saboda a ga yadda zai kawo canjin da mutanen jihar ke bukata.

Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya karbi ragamar iko a lokacin da jihar ke fama da jerin mastaloli wadanda suka hada da bashin da ‘yan fansho da gratuti suke bin gwamnati da ya kai Naira biliyan 29.

Haka ma zargin da ya yi na samun aljihun gwamnati babu kudi da ma sauransu.

An samu cigaba wurin samar da ababen more rayuwa a jihar wadanda suka hada da ginin hanyoyi a kauyuka da ma birane da kuma ginawa da sake farfadowa da daruruwan makarantun firamare da sakandare.

A hadin gwiwarta da Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da kungiyar Plan International mai yaki da talauci, da sauran kungiyoyin raya kasa daban-daban, gwamnatin ta gina da kuma farfado da cibiyoyin kiwon lafiya a mazabu 43.

A bangaren ilimi, gwamnatin ta gina azuzuwa 270 inda ta farfado da guda 405 a makarantun firamare da sakandare a jihar

Duk da wadannan nasarorin, Gwamna Bala Mohammed ya gaza cika alkawarin da ya yi na gudanar da zabubbukan kananan hukumomi cikin watanni shida na farkon mulkinsa kamar yadda ya alkawarta wa al’ummar jihar.

Nasarawa

A nashi bangaren, Gwamna Abdullahi Sule ya karbi mulki a jihar Nasarawa da kudurin ba da muhimmanci ga matsalar tsaro wadda sassan jihar suka dade suna fama da ita.

A kokarinsa na farko a wannan bangare, Gwamna Sule ya sa rundunar sojin sama ta kafa sansaninta a filin jirgi da ke birnin Lafia.

Ya kuma ba da damar kafa wasu matakan tsaro da dama tare da hadin gwiwar ‘yan sanda.

A ‘yan kwanakin nan ya kai ziyara Fadar Shugaban Kasa, inda ya tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari a kan batutuwan da suka shafi tabarbarewar tsaro saboda lalubo hanyar magance su.

A bangaren samar da ababen more rayuwa, gwamnan ya sanya hannu a kan kwantiragin gina hanya mai tsawon kilomita 15 a yankin Sisin Baki zuwa Farin Ruwa.

Ya kuma gina azuzuwa, da tashar manyan motoci a karamar hukumar Karu da kokarin mayar da ‘yan kasuwar bakin hanya zuwa babbar kasuwa da aka sanya wa sunan Muhammadu Buhari.

Da yake tsokaci a kan shekara daya da gwamnan ya yi a mulki, shugaban jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Francis Orogu. ya ce, “Muna ganin natsuwa da kuma kokarinsa amma ya kamata mu samu fiye da haka”.

Kwara

Shi kuma Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq, ya taka rawar gani a cikin shekara daya da ya yi musamman a bangarorin kiwon lafiya, da noma da kuma samar da ababen more rayuwa.

Wasu daga cikin nasarorinsa sun hada da kokarin farfado da makarantu 31 a fadin jihar.

A bangaren kiwon lafiya, Gwamna Abdulrasaq ya kashe Maira miliyan 232 saboda magance zazzabin cizon sauro, rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara da kuma mutuwar mata wurin haihuwa.

Gwamnatin ta kuma gina cibiyoyi biyar saboda yaki da cututtuka masu yaduwa.

Sabuwar gwamnatin ta jihar Kwara ta kuma sayo motocin daukar marasa lafiya guda biyar wadanda suke dauke da na’urorin taimaka wa marasa lafiya numfashi.

Sauran bangarori da ayyukan suka shafa sun hada da asibitin kwararru na Sobi, da asibitin ido da kuma kwalejin koyar da ilimin kiwon lafiya da ke Offa.

A bangaren noma, gwamnatin ta gina babbar hanya daga Maigida zuwa Bani saboda samar wa manoma hanyar kai kayakin amfanin gonarsu zuwa kasuwa.

Ya zuwa dai gwamnatin ta gina hanyoyi 68 duk da cewa akwai wadanda ba a gama ba.

Legas

Tun lokacin da ya karbi iko daga hannun tsohon Gwamna Akinwumi Ambode a watan Mayu na shekarar 2019, gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta ke fama da kwan-gaba-kwan-baya.

Duk da haka, gwamnan ya yi azama inda ya gudanar da ayyuka da dama a bangarorin tsaftace tituna, sufuri, kiwon lafiya, muhalli, ilimi da fasaha inda ya mayar da jihar kan gaba ta fuskar tattalin arziki, nishadi, yawon bude ido, tsaro da gudanar da mulki nagari.

Daya daga cikin bangarorin da ya fi mayar da hankali shi ne dawo da martabar hanyoyi a jihar da kuma samar da hanyar rage cunkoson ababen hawa a yankunan jihar.

A yunkurinsa na ganin hakan, gwamnan ya rattaba hannu a kan kudurin dokar da ta bai wa Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa a Jihar (LASTMA) karfin tabbatar da doka da kuma kara wa ma’aikatanta albashi da kuma lokutan aiki.

Duk da kokarin da gwamnan yake yi tare da mataimakinsa, Dokta Obafemi Hamza, suna fuskantar koke-koke dangane da wasu hanyoyi wadanda mafi yawan mazauna jihar suke tunanin su ne suke jawo cunkoson ababen hawa.

Ita kuwa gwamnatin ta dora alhakin matsalar a kan yanayin damuna na gaza gyara hanyoyin wanda bayan wucewar damuna ta kaddamar da aikin hanyoyin wanda ya kawo saukin cunkoso a jihar.

Gwamnan ya kuma kammala wasu ayyuka da gwamnatin da ta gabace shi ta faro wadanda suka hada da gadar sama da ke Agege, tashar manyan motoci da ke Abule-Egba/Oshodi, babbar hanyar Legas zuwa Badagry da sauransu.

Gwamnatin ta Sanwo-Olu ta debi malamai 10,000 saboda karfafa makarantun firamare da sakandare a jihar

Daya daga cikin rawar da gwamnan ya taka da ya jawo hankula sosai shi ne dakatar da ‘yan acaba a jihar.

Hakan ya jawo suka daga bangarori da dama luma zuwa yanzu ba a gama shawo kan rikicin da hakan ya haifar ba.

Duk da haka, masu sa ido a kan lamura sun bayyana cewa gwamnatin Sanwo-Olu ta nuna kwarewa da kuma iya gudanar da mulki.

A yayin da jam’iyya mai mulki ta yaba masa, ita kuwa jam’iyyar adawa ta bayyana rashin gamsuwarta game da rashin bayyana abubuwa a fili a yayin raba tallafi saboda rage tasirin dokar kulle da aka sa.

Mutanen jihar ta Legas za su ci gaba da sa ido a sauran shekaru masu zuwa domin ganin kokarin da gwamnatin za ta yi a bangaren samar da aikin yi da sauran ababen more rayuwa.

Oyo
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bai wa al’ummar jiharsa tabbacin mai da hankali wurin biyan albashi a kan kari, abin da ma’aikata a jihar suka dade suna fatan samu.

A bangaren tituna, sabuwar gwamnatin ta soma ginin hanyar Iseyin zuwa Ibadan saboda samar da wata kafa ta isar da amfanin gona zuwa birnin.

Jim kadan bayan rantsar da shi, gwamnan ya karbi bashin biliyan 7 da miliyan dari 6 saboda inganta sanannun wuraren noma biyu a jihar wadanda suka hada da Akufo da Eruwa wadanda har zuwa yanzu ba su kankama ba.

Zuwa yanzu dai babu wani cigaban a zo a gani a bangaren ilimi duk da sanar da janye karbar naira dubu daya a matsayin kudin makaranta daga hannun yara a makarantun gwamnati.

Masu sharhi sun bayyana cewa sauran bangarori da suke bukatar sa hannun gwamnan sun hada da tsaro, kiwon lafiya da tattalin arziki.