Da Dumi Dumi

Rayuwa za ta iya canjawa cikin lokaci kalilan – Ummi Zee Zee

Ummi Zee Zee

Fitacciyar tsohuwar jarumar Fina-finan Hausa na Kannywood, Ummi Zee Zee ta bukaci mutane su zauna da juna lafiya tare da rike addu’a da sadaka da istigfari domin samun nasarar rayuwa Ummi Zee Zee ta bayyana haka ne a wani sakon da ta aike wa masoyanta a shafinta na Instagram inda take cewa, “Rayuwa za ta iya canja maka a cikin mintuna kalilan. Abin da ka saba da shi zai iya sauyawa zuwa wanda ba ka taba tunani ba. Bakin ciki ko farin ciki, rashi ko samu. Allah Yana jarabtar bawa ta kowane fanni. Kada ka taba dauka kai kadai ne a yayin da duniya ta yi maka kunci,” inji ta.

Ummi ta kara da cewa komai ya faru da kai jarrabawa ce daga Allah, inda ta ce “Idan abu ya faru da kai, jarrabawa ce Allah Ya dora maka don Ya ga karfin imaninka gare Shi. Ka zama mai tawakkali da addu’a,  za ka ga sakamakon hakan. Ba lallai ya faru a lokaci daya ba, kada ka gaza. Ka rike addu’a da sadaka, ka kyautata imaninka. Ka yawaita istigfari da Salatin Annabi, kuma ka mika lamuranka ga Allah.  Allah Ya sa mu dace, amin.”

Share