✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar almajirai: ‘Ba ma jin dadin kyarar da ake nuna mana a Jos

Wadansu yara su biyar da shekarunsa ba su wuce shida zuwa tara ba, kowannensu rike da robar bara ne suke ta gagaramba a kusa da…

Wadansu yara su biyar da shekarunsa ba su wuce shida zuwa tara ba, kowannensu rike da robar bara ne suke ta gagaramba a kusa da wasu bankuna da ke Titin Ahmadu Bello daura da Kasuwar Terminus a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Yaran kafafunsu ko takalma babu duk da tsananin zafin ranar da ake yi, kuma tufafinsu suna nuna cewa suna cikin mawuyacin hali. Sun yi fari fat kamar wadanda aka yi wa wanka da gari, abin da ke nuna sun dade ba su yi wanka ba.

Duk mutumin da suka hango sai su ruga da gudu wurinsa suna rokon ya ba su kudi su sayi takalmi ko wani abu daban. Wadansu sukan ba su kudin, yayin wadansu ke daka musu tsawa ko su ki sauraronsu. Ko an ba su kudi ko ba a ba su ba hakan ba ya sa almajiran su daina barar.

Aminiya ta gano cewa ba ya ga bara a gidajen mutane don neman abinci, wadansu na zuwa bakin bankuna da kofofin shiga manyan ma’aikatu da makarantu don yin bara.

Aminiya ta gano yawancin dakunan da almajiran suke kwana ba ma su kyau ba ne, inda wasu dakunan babu marufin tagogi ko kofofi, sannan babu ban-dakuna masu tsabta.

Wani almajiri mai suna Ahmad Ibrahim, dan shekara takwas da aka turo shi almajiranci daga wani kauye a Karamar Hukumar Funtuwa da ke Jihar Katsina ya bayyana wa Aminiya cewa yakan yi barar abinci ko kudi duk lokacin da suka tashi daga karatu.

Ya ce ta hanyar barar ce yake iya biya wa kansa wasu bukatu har ma ya kai wa malaminsa kudin da aka dora masa. Ya ce, idan zai yi barar kudi ne yake zuwa Kasuwar Terminus, idan zai yi ta abinci kuma sai ya je gidajen mutane. “Nakan zo bara nan Kasuwar Terminus ne duk lokacin da muka tashi daga karatu don in nemi kudi, a nan nake samun kudin sayen abinci da wanda zan kai wa malamina da ke Unguwar Rimi. “An dora mini in kai Naira 50 kowace rana, inda wani lokaci nakan samu fiye da Naira 50 din, wani lokaci kuma in koma hannu rabbana,” inji shi.

Ya ce, sun kai kusa su 200 a tsangayarsu da ke Unguwar Rimi, kuma dakunan da suke kwana babu marufin tagogi ko kofofi. Kuma ya ce an turo shi almajirci ne tun yana dan shekara shida, kuma kafin zuwansu Jos a bara sun zauna a Gombe.

Shi kuwa almajiri Muhammad Haruna, dan shekara 10 daga Daura a Jihar Katsina ya ce kimanin shekara hudu ke nan yake almajirci, kuma a yanzu yana da haddar izu 20. “Rayuwar almajirci akwai wahala, amma da ma neman ilimi sai an sha wahala. Na fara almajirci yau shekara hudu, kuma ina da haddar izu 20 yanzu. Nakan fita bara ce don in samu abin da zan ci in biya wa kaina sauran bukatu, domin malaminmu ba ya aikin komai sai koyar da karatu, wani lokaci ma mu muke kai masa kudi ko abinci,” inji shi.

Almajirin wanda makarantar allonsu ke Kwanar Shagari a Jos ya ce, babu abin da ke yi masa ciwo kamar kallon kaskanci da wadansu suke yi musu maimakon su daraja su saboda karatun Alkur’anin da suke yi.

Mustapha Isah almajiri mai shekara 15 ya shaida wa Aminiya cewa shi ba ya bara, daga ya tashi daga karatu sai ya dauki kayan aikin gyaran takalmansa ya nufi cikin gari don yin aiki, kuma cikin ikon Allah yana samun abin da yake iya biya wa kansa bukatu.

Mustpaha ya ce tabbas almajirai na cikin wani hali inda ake kyararsu, ake ganin su ne suke zama ’yan Boko Haram ko wadansu batagari, amma kuma gwamnati ta ki tashi tsaye don ganin ta kawo musu tallafi.

Wani malamin tsangaya mai suna Malam Harisu Idris ya bayyana wa Aminiya cewa a dole almajiransa suke bara, ba don yana so ba, saboda bara kaskanci ce.

Ya ce, “A dole almajiraina suke bara, babu yadda zan yi ne, don haka ne ma nake kira gwamnati ta shigo cikin batun makaratun allo da na tsangaya, ta tallafa musu domin su ma ’yan Najeriya ne.”

Ya shawarci gwamnatoci su samar da ma’aikatu a jihohin Arewa da za su rika lura da makarantun allo da na tsangaya don almajirai su samu ilimin boko da na addini da kuma na kananan sana’o’i don su iya dogara da kansu.

Binciken Aminiya a daya daga cikin makarantun Tsangaya da gwamnatin Goodluck Jonathan ta gina a Pebuna da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a sherarar 2014, ya gano an gina makarantar ce ba tare da ban-daki ko dakunan kwanan almajirai ba. Makarantar tana da ajujuwa uku inda a yanzu take da dalibai kimanin 500.

Malamin Tsangayar, Malam Ibrahim Adam Salihu ya bayyana wa Aminiya cewa “An gina tsangayar ce lokacin Jonathan a 2014, ginin kawai aka yi amma babu wani tallafi da aka ba mu, an gina ajujuwa uku, wurin kwana kuma mu ne muke ta kokarin nema har yanzu, hatta ban-daki, ni da sauran daliban makarantar muka hada kudi muka gina.”

Ya ce, a lokacin da aka fara karatu a tsangayar, “Ni da sauran almajirai muke hada kudin da muke biyan malaman boko, abin da almajiran suka hada idan wata ya yi sai in cika a biya, inda a yanzu da rayuwa ta yi tsada sai muka janye aka daina karatun bokon,” inji shi.

Ya ce, a yanzu tsangayar tana dauke da almajirai 500 wadanda suka hada da ’yan gari da kuma wadanda ba ’yan gari ba.  “Ka san makarantar tsangaya juyi-juyi ce da rani in an kammala noma akwai akalla dalibai ’yan gari da wadanda ba ’yan gari ba kamar 500. Idan damina ta yi yaran sukan koma gida, manyan cikinsu su koma su yi noma, wadansu su su taya iyayensu aiki. Da damina dalibaina ba sa wuce 200 ko 100,” inji Malam Salihu.

Ya ce manyan almajiran sukan je garuruwansu su yi noma, “A cikin amfanin gonar ne suke sayarwa su sayi sutura, su taho da sauran zuwa tsangayar, inda za su ajiye su rika dafawa da safe da rana da daddare. A cikinsu akwai masu gyaran takalma da yari da gyaran farce da sauran aikin hannu da kananan sana’o’i, da suke fita ranar Alhamis da Juma’a da ba a karatu, kudin da suka samo sai a yi cefane, kananansu ne kawai suke fita su yi bara,” inji shi.

Ya ce ba ya dora wa dalibansa cewa dole kowa sai ya fita ya nemo kudi, a tsarinsa manyan almajiran ne suke daukar nauyin kansu, “Ni ma ni nake daukar nauyin kaina, ina yin noma da kiwo, shi nake rike kaina da shi,” inji shi.

Ya ce,sun kafa asusun da suke ajiye kudi, saboda idan an samu rashin lafiya ko wani abu na ba-zata sai su magance shi. “Kananan almajirai kowa zai ba da Naira 10 duk karshen mako, yayin da manyan kuma Naira 20. Almajiran ne suke tarawa su ajiye kudin,” inji shi.

Ya ce, abin takaici shi ne gwamnati ta daina agaza wa tsangayarsa tunda aka gina ta, inda hatta fentin tsangayar shi da almajiran ne suka yi da kudin da suke tarawa.

Malamin ya ce, “Wadansu daga cikin daliban suna kwana a ajujuwa uku na makarantar, inda aka raba aji kashi biyu, wurin karatu da wurin kwana, ana shimfida musu tabarmi. Sannan akwai wanda ya ba mu gida dalibai suna kwana, haka gaba kadan da makarantar akwai wasu gidaje da aka ba dalibai suke kwana.”

Ya ce in da tsarin da gwamnatin Jonathan ta dauko ya dore maganar bara da ake yi yanzu da an daina, “A yanzu misali akwai takin zamani da wurin kwana, za mu je da yaran gona mu yi noma, to mu da kanmu za mu rika daukar nauyin kanmu, domin za mu iya noma mu sayar da amfanin gonar mu biya bukatunmu,” inji shi.

Ya shawarci gwamnati ta samar da malaman da za su rika koyar da ilimin boko a makarantar don su rika koyar da almajiran inda za su samu damar hada ilimin zamani da na addini. Kuma ya ce ya kamata gwamnati ta rika koyar da almajiran kananan sana’o’i maimakon su tafi bara.

Malam Ibrahim ya ce ya fi shekara 30 yana koyar da almajirai, kuma ya zauna a garuruwa daban-daban, kuma har yau babu wani daga almajiransa da ya zama mutumin banza.

Ya ce, bayan gina tsangayarsa a shekarar 2014, an dauki matan da za su rika dafa abinci ga almajiran, amma abin bai dore ba, “Kuma da ma ba zai dore ba, idan ana so abin ya dore sai a fitar wa da almajiran ayyukan da za su rika yi idan sun tashi daga karatu,” inji shi.

Da wakilinmu ya tuntubi Hukumar Ilimin Bai-Daya ta Jihar Filato ta ce ba ita ke da hakkin tura malamai ko ba almajiran makarantar abinci ko samar musu dakin kwana ba.

Kakakin Hukumar Mista Richard Jonah, ya ce dukan abubuwan da aka yi korafi a kansu hakkin Gwamnatin Tarayya ce wadda ta samar da makaratun, su dai an dora hakkin lura da makarantar a hannun hukumarsu ne.

“Ba mu ne muke da hakkin ba su wurin kwana ko abinci ko malaman da za su rika karantar da su boko ba, shiri ne na Gwamnatin Tarayya, mu dai an ce mu lura komai ya tafi daidai ne, kuma zuwa yanzu komai ya tsaya,” inji Mista Jonah.

Ya ce kamata ya yi a tuntubi Gwamnatin Tarayya dangane dabatun makarantun Tsangayar da aka gina a kasar nan.

 Malam Shehu Mai ‘Yan makaranta
Malam Shehu Mai ‘Yan makaranta

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Malam Shehu Sulaiman wanda aka fi sani da Malam Shehu Mai ‘Yan makaranta kuma Mai unguwar Ibrahim Katsina da ke garin Jos, kuma shugaban masu unguwannin Hausawa da Fulani na Jos shi ne shugaban Kungiyar Makarantun Allo na Jos, ya ce makarantun allo, su ne rushin Musulunci a Afirka.

Malam Shehu Mai ’Yan makaranta, wanda ya ce ya yi sama da shekara 30, yana rike da shugabancin kungiyar, ya ce a Jos makarantunsu na allo a rubuce suke tuntuni. “Kowace makaranta akwai yawan yara almajirai maza unguwar Ibrahim Katsina da ke garin Jos, kuma shugaban masu unguwannin Hausawa da Fulani na Jos shi ne shugaban Kungiyar Makarantun Allo na Jos, ya ce makarantun allo, su ne rushin Musulunci a Afirka.

Malam Shehu Mai ’Yan makaranta, wanda ya ce ya yi sama da shekara 30, yana rike da shugabancin kungiyar, ya ce a Jos makarantunsu na allo a rubuce suke tuntuni. “Kowace makaranta akwai yawan yara almajirai maza da mata da yawan malaman makarantar a rubuce tun a wancan lokaci. A lokacin muna da makarantu kusan 100 kuma kowace makaranta da yawan dalibanta,” inji shi.

Ya ce a 1965 sun tafi wurin marigayi Sardaunan Sakkwato, don su samo tallafi saboda lokacin an fara tallafa wa makarantun allo, sai suka tafi da tsarinsu wani babban jami’i a ofishin Sardauna da yake zagaya lardunan Arewa yana ganin matsalolin makarantun allo, don tallafa musu, mai suna Malam Jimada, ya yi musu alkawarin zai zo Jos don ya duba makarantunmu, amma kafin ya zo, aka yi juyin mulki a 1966.

Ya ce ba za a hada karatun da ake yi da a makarantun allo da yanzu ba. Domin yanzu an rushe karatun allo a Arewa sai kadan suka rage, domin ko Maiduguri yanzu idan ak aje za a ga makarantun allon da aka san da su a da yanzu babu su.  Ya ce a da yana da almajirai maza da mata sama da 700 a gabansa. Kuma a da marantunmun allo a nan Jos lokaci daya suke bayar da hutu, kuma shi ne yake bayar da takardar hutu ga dukan makarantun allon na Jos.

Malam Shehu Mai ’Yan makaranta ya ce a yanzu suna da makarantun allo 60 a Jos, amma ba su samun taimakon komai daga gwamnati. Sai dai daga mutane da suke son a yi musu addu’a da suke zuwa su ba da sadaka su ce a sauke masu Kura’ani, a yi musu addu’a. Sai kuma kudin Laraba da suke karba Naira 50 daga kowanne yaro.

“Babbar matsalar da muke fuskanta yanzu ita ce iyayen yara ba su cika damuwa da karatun allo ba. Domin za ka samu malami yana da yaro 100, idan Laraba ta zo da wuya ka ga ya samu kudin Laraba,” inji shi. Ya ce  an gina musu makarantar tsangaya a Jos da Mangu a zamanin gwamnatin Jonathan

Malam Mai ’Yan makaranta ya ce makarantun allo a Afirka su ne tushen Musulunci. Domin ta hanyar makarantun ne ake karantar da Alkur’ani a haddace shi a rubuta shi. “Sauran makarantunmu na zamani za ka haddace izu 20  amma ba za ka iya rubuta izu 1 da ka ba. Don haka makarantun allo suna matukar mahimmanci,” inji shi.

Ya ce kada al’ummar Musulmi su bari karatun allo ya mutu a kasar nan, su rika kokari suna karfafa wa ’ya’yansu gwiwa, wajen yin karatun allo, wanda ya ce ba zai hana yin karatun zamani ba. “Akwai manyan ma’aikatan gwamnati a wurare daban-daban da a wurina suka yi karatun allo har suka sauke,” inji shi.