Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Rayuwar Duniya: Labarin Malam Shagalalle (3) - Aminiya
Aminiya

Rayuwar Duniya: Labarin Malam Shagalalle (3)

Assalamu alaikum, ya ma’abota karatun wannan fili na Sinadarin Rayuwa. A makonni biyu da suka gabata ne muka fara kawo muku wannan labarin. Duk da cewa mun koro labarin amma dole ta sanya muka tsagaita, ga shi za mu ci gaba a wannan makon da yardar Allah, kamar haka:

Ya zuwa lokacin da ya ga matar nan ta tsaya a bakin wata makabarta, sai rana ta fadi. Daga nan ya fara tunanin cewa, shin ko shi ma ya haukace ne? Yaya za a ce yana bin mace tun daga Azahar har ga shi rana ta fadi, amma bai fasa bin ta ba? Amma duk da wannan tunani da yake yi, bai tsaya ba, ya ci gaba da tafiya zuwa shiyyar matar nan da nufin isa wurinta.

Mutumin ya ci gaba da tafiya har ya kusa iske matar nan, saura bai fi taki biyar ya isa wurinta ba, sai kawai ta ci gaba da tafiya. Yana gani ta tura kyauren makabartar nan ta shiga ciki. Maimakon ya tsorata ya dawo baya, amma dai abin da ya kama zuciyar mutumin nan na kyawun jikinta ya kara rudarsa, sai shi ma kawai ya tura kyauren ya shiga cikin makabartar, yana bin bayanta.

Mutumin ya lura da inda matar nan ta shiga, ta shiga wani rami ne wanda ke da matakalai da yawa a kasa, kuma daga nesa ya hango cewa akwai haske da ke fitowa daga ramin, wanda yake zaton kamar ma daki ne ko kuma zaure mai dan fadi. Ba tare da wani tunani ba, sai mutumin nan ya bi matar zuwa cikin ramin, ya tattaka matakalun zuwa kasa, ya wuce zaure na farko, ya isa zaure na biyu, ya ga yana da kyaure. Bai tsaya ba sai kawai ya tura kyauren, ya bude kuwa. Kawai sai ya sanya kai zuwa cikin dakin da nufin ganin kwakwaf, na ina matar nan ta shiga?

Yana shiga ciki sai ya samu kansa cikin wani faffadan daki mai yalwa, wanda hasken fitilun kyandirori ya cika shi ko’ina. A gefen kuma jikin bangon sai ya ga wannan mata da ya biyo, tana zaune kan wata shimfidar alfarma, ta tada kai da wani matashin kai mai inganci da kyawun kwalliya. Matar kuma tana cikin kwalliyar suturun nan bakake da take sanye da su tunda farko, wato ba ta ma canja kaya ba ke nan. Daga bangaren dama na dakin, mutumin nan ya lura da wata rijiya.

ADVERTISEMENT

“Rufe kofar da ka shigo sannan ka kulle ta da makullin nan da ke jikin kuba.” Haka matar ta gaya masa cikin wata tausassar murya mara karfin sauti. Muryar tata kamar tana yi masa rada ne, shi kuwa ya juya ya kulle kofar, ya tsaya yana jiran umarni na gaba; a yayin da ya maida fuskarsa ga matar nan, yana kallonta.

Ganin haka sai matar nan ta yi masa ishara da rijiyar nan, wacce ga dukkan alamu take da zurfi sosai, kuma tana dauke da ruwa kandami. “Jefa mabudin nan na hannunka cikin rijiyar nan.” Abin da ta gaya masa ke nan. Shi kuma sai ya yi tsaye sototo, ya sha jinin jikinsa. Ya kara kankame mabudin nan a hannunsa, ya ki jefawa.

Za mu ci gaba