Search
Subscribe
Rayuwar sai da ilimi  mata – Samira Ibrahim

Samira Ibrahim

Rayuwar sai da ilimi  mata – Samira Ibrahim

Hajiya Samira Ibrahim ’yar asalin garin Zuru da ke Jihar Kebbi, tsohuwar malamar makaranta ce, kuma tsohuwar ’yar jarida, yanzu kuma Babbar Daraktar a Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar Kebbi. A zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da gwagwarmaya da ta sha:

Tarihin rayuwata:

Sunana Samira Ibrahim. Ni ’yar asalin garin Zuru ne a Jihar Kebbi, an haife ni a garin Sakkwato a 1981. Na fara makarantar firamare ta Mabera a garin Sakkwato sai mahaifinmu Alhaji Ibrahim Magajin Garin Zuru, Allah Ya yi masa rasuwa, daga nan sai muka koma garinmu Zuru, domin dama aikin gwamnati ya kai mahaifinmu can. Daga nan sai muka dawo Sakkwato da ni da mahaifiyata, a nan na kare makarantar firamare.

Ina gama firamare ba da dadewa ba sai Allah Ya yi wa mahaifiyarmu rasuwa a can, daga nan sai na dawo gida Zuru, inda na fara makarantar sakandare ta Gobenment Day, Zuru a 1993, wanda ake kira yanzu da Sakandaren Bahago Gomo.

Bayan na kammala sakandare ina nan Zuru sai yayata ta tafi da ni Legas inda na je na fara koyon dinki. Bayan na shekara uku a Legas sai muka sake dawowa Sakkwato inda na shiga makarantar da ake kira Halliru Binji College of Arts na yi Difloma a sha’anin mulki.

Da na kammala Difloma sai na fara aikin malanta a Attahiru Dalhatu Bafawa Model Primary School a garin Sakkwato, a cikin wannan shekara da na fara koyarwa ni ce na dauki ta farko a cikin malaman makarantar. Ina cikin koyarwa sai na tafi Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato a shekarar 2003 inda na yi digiri na farko na gama a 2006 daga nan sai na wuce hidimar kasa. Bayan na gama sai aka yi mini aure aka kawo ni Birnin Kebbi daga Sakkwato, kuma dama jihata ce domin ni mutuniyar Zuru ce.

Bayan na yi aure sai na shiga Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi domin in yi Babbar Difloma a kan malanta, domin a rayuwata har gobe ina da sha’awar koyarwa.

Bayan na yi Difloma karama da babba, na yi digiri na farko sai na fara aiki da gidan rediyon Jihar Kebbi a sashen shirye-shirye da kuma labarai, daga nan sai aka canza ni zuwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, ina nan wannan hukuma sai na sake zuwa makarantar Kimiyya da Fasaha ta Waziri Umaru domin yin wata babbar Difloma a kan sha’anin mulki wanda ake yi tare da hadin gwiwar Jami’ar Usman Danfodiyo.

Daga nan sai aka tura ni Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kebbi a matsayin Daraktar Mulki, ina wannan ma’aikata sai na nemi izinin zuwa jami’a domin in yi digiri na biyu wato masters, amma sai wurin aikina suka ce tunda Sakkwato ne zan yi digirin na biyu sai dai su tura ni ofishinmu da ke Sakkwato wato Laision Office in rike wurin har in kammala karatuna.

Bayan na gama na dawo sai aka tura ni Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kebbi, daga nan sai aka dauke ni zuwa Ma’aikatar Harkokin Mata da Marayu, ban dade a wannan ma’aikata ba sai aka canja ni zuwa Ma’aikatar Aikin Gona a matsayin Babbar Daraktar Mulki inda har yanzu da nake magana da kai ina wannan ma’aikata.

Kalubale:

Kalubale da zan ce na samu a wuraren da na yi aiki shi ne gidan rediyo da na zauna, domin a kullum sai na je neman labarai kuma ni zan sa wa motata mai kuma ni zan sayi kaset da zan yi aiki da shi. Lallai sai na ga cewa wannan aiki ba ka karuwa sai raguwa. Na farko dai babu hutu kuma komai kai za ka yi wa kanka, hatta ranar Sallah ranar hutun kowa kai kana aiki. Kuma na san gwamnati tana iya bakin kokarinta wajen ba da kayan aiki amma mu ba su zuwa gare mu.

Abin da na so zama lokacin da nake karama:

Abin da na fi sha’awa shi ne tukin jirgin sama, amma Allah bai Yarda ba, kuma daga baya sai na rika jin ana cewa mai aikin jirgi kamar lebura yake, daga nan sai ya fita a raina. Amma kuma sai aikin koyarwa ya shiga min rai har yanzu kuma yana cikin raina domin ina sha’awarsa ba don komai ba sai saboda aikin koyarwa yana kara bude wa mutum kwakwalwa.

Burina:

Burina shi ne in ga na kai matsayin dakta ko farfesa, domin ko yanzu zan koma makaranta in yiwo digiri na uku in Allah Ya yarda. In ga na gama aikin gwamnati lafiya, kuma idan mutuwa ta zo in cika da imani. Domin babu wani buri ga ma’aikacin gwamnati illa ya gama aiki lafiya.

Darussan da na koya a rayuwa:

A kullum mutum ya kasance ya rika shuka abu mai kyau domin samun sakamako mai kyau, ko Musulmi ko Kirista yana da kyau ya yi abu mai kyau a rayuwa domin samun sakamako mai inganci. A zama masu dogaro da Allah a duk lamarin da mutum ya tsinci kansa. Kada a ga mai kudi sannan a ce dole sai an yi irin wannan kudi. Haka ya kamata rayuwa ta kasance, kuma kada a rika damuwa da abin da wadansu ke fadi a kanka domin Allah kadai ne Ya san masu aikata mummunan abu.

Tarbiyya daga iyaye:

A gaskiya iyayena sai dai in ci gaba da yi musu

addu’ar Allah Ya saka musu da alheri. Domin a kullum suna yi min huduba cewa duk inda nake in zama mai hakuri, kuma duk yadda na ga mutum in mutunta shi, in ya girme ni in ba shi girman da Allah Ya ba shi. Sukan ce min kada in zama mai wulakanta jama’a a duk irin mukamin da na samu kuma in rika daraja mutum babba ko karami.

A kan haka ne duk ma’aikatar da na je za ka ga ina mu’amala da jama’a kuma da zarar an canja ni daga wannan ma’aikata za ka ga jama’ar da muke aiki da su ransu ya baci. Ba komai ne ya jawo min haka ba illa tarbiyyar iyaye da na dauka tun ina karama.

Haka ita ma kakata ta ba ni gagarumar gudunmawa wajen ganin na samu kyakkyawar tarbiyya saboda na dan zauna da ita.

Sakona ga mata:

Mata ku tashi ku nemi ilimi domin ilimi na gaba da komai a rayuwa. idan aka ce ilimi ana nufin ilimin addini da na zamani. Idan mace tana da ilimi za a rika damawa da ita a rayuwa a kowane fanni, musamman a aikin gwamnati da bangaren siyasa ko kasuwanci. Sannan mace mai ilimi ta fi wacce ba ta da ilimi daraja, ko a rayuwar aure ne.

Sannan ina kira ga iyaye su guji dora wa ’ya’yansu musamman mata talla, don talla wata hanya ce ta lalata tarbiyya. Idan suka tarbiyyantar da ’ya’yansu za su ci gajiyarsu a lokacin da suke raye da kuma bayan rayuwarsu.

Kasashen da na je:

Na je Saudiyya da Mali da Nijar da Kenya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin