✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuwar ’yan acaba a Abuja

Sana’ar Acaba da a baya aka dauke ta a matsayin ta rufin asiri, ta zama babban abin dogaro da kai a yanzu, musamman ga ’yan…

Sana’ar Acaba da a baya aka dauke ta a matsayin ta rufin asiri, ta zama babban abin dogaro da kai a yanzu, musamman ga ’yan Arewa da dama.

A farkon bayyanar sana’ar a Abuja, wadansu daga cikin kananan kabilun Arewa maso Tsakiya ne da na Kudancin kasar nan ke gudanar da ita, sai dai a yanzu al’ummar Hausawa musamman daga jihohin Arewa maso Yamma sun karbe ragamar gudanar da harkar a Abuja, inda Jihar Katsina ke kan gaba.

Jama’a da dama suna da ra’ayin cewa hakan bai rasa nasaba da yadda gwamnoni da’yan siyasar yankin suka rungumi al’adar sayen babura don raba su ga matasa a matsayin karfafa samar musu da sana’a. Akwai kuma matsalar rashin tsaro da rashin abin yi a yankunan, lamarin da ya tilasta wa wadansu masu sana’ar hijira zuwa Abuja. Hakan na ci gaba da karuwa duk da dokar hana acaba ko hawa babura a kwaryar birnin, da ta faro aiki a lokacin tsohon Ministan Abuja Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, inda aka takaitata sana’ar babur a yankuna da ke wajen birnin kawai.

Aminiya ta zanta da ’yan acaba a garuruwan Kubwa da Nyanya, biyu daga cikin muhimman garuruwan da ke kan manyan titunan shiga Abuja. Maharazu Abdullahi wani matashi dan asalin garin Malumfashi a Jihar Katsina da wakilinmu ya zanta da shi a babbar tashar ’yan acaba ta Unguwar Gbazango Kubwa, ya ce kashi 3 cikin 5 na masu sana’ar suna karbar baburan ne a tsari na tsawalallen farashi da ake kira da Ingilishi “Hire purchase.”  Ya ce suna amsa ne daga wajen wadanda suka saya, inda suke biyan kudin baburan a hankali har tsawon shekara daya ko sama da haka.

Ya ce ’yan acaba masu babura na kansu ba su wuce kashi 2  cikin 5 ba. Ya ce sabon babur da ake sayarwa a kan Naira dubu 225, iyayen gidansu na ba su a kan Naira dubu 370 zuwa dubu 400 a tsawwalallen farashi. Ya ce a duk mako sukan ba da balas a kan Naira dubu 8 zuwa 10, gwargwadon yadda aka shirya a yarjejeniyar, har a kammala biyan kudin.

Game da ribar da suke samu, ya ce a duk yini bayan sun fitar da kudin mai da na abinci da sauran dawainiya da kuma kudin mai babur, suna tsira da kamar Naira 1,500 zuwa 2,000, a karshe babur din ya zama nasu bayan sun kammala biya. Ya ce idan aka samu akasi barayi ko ’yan sanda ko wata hukuma suka kwace babur, yawanci ana tilasta musu biyan kudin babur din ne  kan wannan tsawalallen farashi, inda a wani zubin sai sun koma gida sun sayar da wata kadara tasu sannan su biya.

Dan acabar ya ce a yanzu sun samu sauki a garin Kubwa wajen kama musu babura da ’yan sanda ke yi kan tsayawa a inda aka haramta kamar gaban banki ko kan kwana, sabanin a baya inda ake kama baburan a ci su tara a nan take, ko a kai su ofishin ’yan sanda. Ya ce a lokacin da ake yawan kama baburan, ’yan sanda na cin su tarar Naira dubu daya nan take, ko Naira dubu biyar idan aka kai babur din ofishin ’yan sanda.

Ya ce a wani zubin wadansu ne da ba su sanye da kaki amma ke rike da bindiga suke kawo musu samame da budaddiyar mota, suna kwace baburansu su tafi da su. “Shi ke nan mun rabu da baburanmu saboda ko mun je ofishin ’yan sanda suna ce mana ba jami’ansu ne ba. Sai dai duk wannan a yanzu ya yi sauki a nan Kubwa,” inji shi.

Kuma ya ce sun samu rangwame a bangaren masu karbar haraji na Karamar Hukumar Bwari da wadansu ke karbar Naira 50 duk yini, baya ga sitika ta shekara-shekara ta Naira dubu daya a madadinta. Ya ce a lokacin wancan tsarin, Naira 20 na tafiya ne ga Karamar Hukumar Bwari, yayin da Naira 30 kungiyarsu ce ke dauka don raya asusun tallafa wa mambobinsu. Ya ce shi ma wannan tsarin ya kau bayan sun yi bore kan rashin yin amfani da kudin yadda ya dace daga bangaren jagororinsu.

Ya ce tsangwama ta ’yan sandan da ta jagororinsu an kawo karshensu ne bayan wata zanga-zanga da suka gudanar lokacin da wani dan sanda ya karya hannun wani abokin aikinsu.

Wani dan acaba mai suna Alkasim Abubakar da ya yi bayani a kan wuraren da suke kwana, ya ce yawancinsu suna kama dakin haya ne kamar su biyar, yayin da wadansu kuma ke kwana a wasu kangon gidajen da ba a kammala ba, wadansu kuma a barandar shaguna ko kafa dakunan baca na kwano ko katako.

Wani matashi mai suna Muhammadu Rabi’u Sabo, wanda dan asalin Albasu ne a Jihar Kano da ke sana’ar acaba a garin Nyanya, Abuja, ya ce babbar matsalarsu ita ce takurarawar da ya ce ’yan sanda ke yi musu, sai kuma kwace daga barayi. Ya ce a ka’ida an ba su damar yin sana’ar daga Gadar Kwanar Karu zuwa cikin garin Nyanya har ya dangana da garin Maraba da ke Jihar Nassarawa.

“Sai dai duk da wannar damar, a wani lokacin sai ’yan sanda su kawo mana samame a daidai lokacin da muke tsaye a gefen titi, muna jiran masu fitowa daga mota, sai su kama mu. A irin haka suna karbar Naira 200 zuwa 500. Idan kuwa suka dangana da ofishinsu sai ka biya tarar Naira dubu daya,” inji shi.

Ya ce hakan na faruwa ne duk da harajin Naira 50 da suke biya ga Karamar Hukumar Birni da Kewayen Abuja (AMAC) a kullum. Ya ce har ila yau jami’an da ke karbar harajin na sake dawowa da maraice, inda suke cin tararsu Naira dubu daya ga duk wanda ya gaza nuna tikitin harajin da aka biya da rana.

A bangaren barayi kuwa, ya ce yawanci matsala ta fi faruwa da su ne idan suka dauki mutum biyu ko mutum guda amma ya bukaci sauka a inda abokan satarsa suke tsaye a wurin da ba mutane, inda suke daba musu makami ko su fesa musu wani sinadari.

Wadansu masu sana’ar acabar da aka zanta da su, sun yi zargin cewa wasu baburansu da aka kwace ana kai su wani ofinshin BIO da ke Wuye Abuja, tare da cin tararsu har Naira dubu 30. Sai dai ya ce tarar ta hada har da kudin wasu kayan aiki da ake ba su, kamar rigar jaket da hular kwano da lambar babur da kuma lasisin aiki.

Sai dai sun ce matukar aka kai babur zuwa wani sansanin BIO da ke wani dajin kauyen Gosa, sukan fidda tsammanin sake mayar musu da su. Sun yi zargin cewa hukuma na gwanjatar da baburan da ta kai wajen ga wadansu dillalai da suke hulda da su a wulakantaccen farashi.

Aminiya ta kuma zanta da masu sana’ar tuka Keke-NAPEP, wadanda hukuma ta ba su damar gudanar da sana’arsu a gundumomi masu daraja ta biyu. Misbahu Abdullahi wani dan asalin garin Daura a Jihar Katsina, ya ce a bangaren Keke-NAPEP ma, ’yan Jihar Katsina ne suka fi yawan masu gudanar da su a Abuja. Kuma ya ce su ma a bangarensu kamar kashi biyu cikin biyar ne na masu sana’ar ke da na kansu, yayin da kashi uku cikin biyar suke karbarsu a tsawwalallen farashi.

Ya ce sabon keken har da hidimar yi masa lamba da sauransu yana kai Naira dubu 680 a farashin kasuwa. Sai dai a cewarsa a tsarin na “Hire purchase” ana ba su ne a kan Naira miliyan daya da dubu 100 zuwa da 200. Ya ce a duk mako suna ba da Naira dubu 15 zuwa 20, gwargwadon adalcin maigida.

A bangaren samu kuwa, ya ce a duk yini bayan an sha mai da abinci tare da fitar da kudin balas, sukan ajiye nasu kama daga Naira 3000 zuwa 5000, gwargwadon yadda kasuwa ta kasance.

Ya ce hakan na faruwa ne a lokacin da ingancin kekunan ya ragu, adadin masu sana’ar ya karu, sannan harkoki suka ragu, amma ba a rage musu kudin balas. “Sai dai abu guda da zan ce mun samu sauyi mai ma’ana shi ne, cin zarafin da jami’an hukuma suke yi mana ya yi sauki. A gwamnatin baya kana tsaye a nan tasha inda aka yarda mu dauki fasinja sai kawai jami’in tsaro ya kutso wajen ya ci zarafinka, wani zubin har ya fasa maka gilashin keke.

“A baya BIO sun taba kwace mini keke, kuma shi ke nan ya tafi ke nan. Akwai kuma lokacin da aka kama min keke, sai da na yi belinsa a kan Naira dubu 50 daga aljihuna. Abokina kuwa da tasa ta bata, maigidansa ya ki amincewa har aka kai shi gidan yari. Da gwamnatin nan ta zo ne ta sa duk aka fito da kamammun kekuna, aka bai wa masu su. A yanzu idan ka bi dokar yin aiki a iya wuraren da aka yarje mana, ba ka da matsalar hukuma,” inji shi.

Aminiya ta zanta da Babban Daraktan Hukumar Tabbatar da bin Ka’idar Ababen Hawa na Birnin Tarayya Abuja, Malam Wadata Aliyu Bodinga, inda ya yi bayani kan yadda suke gudanar da aikinsu, daga bisani ya sa aka kai wakilinmu zuwa sansanin ajiye ababen hawa da hukumar ta kwace da ke dajin Gosa, Abuja.

Ya ce dokar hana acaba a kwaryar birnin ta biyo bayan yawaitar haddura ne da kuma haddasa cunkaso a hanya da ya ce masu baburan ke haddasawa a birnin sakamakon rashin bin ka’idar tuki. Ya ce an yi haka ne don kare rayukan su kansu masu baburan da na sauran jama’a da ke amfani da titunan.

Haka ya ce su kansu masu kekuna masu kafa uku an kayyade musu wuraren gudanar da sana’arsu, sai dai duk da haka ana samun wadanda ke karya ka’ida, inda suke shiga yankunan da aka hana su yin aiki. Kuma ya ce ire-irensu ne suke kamawa daga bangaren masu babura da kuma keke.

Babban Daraktan ya yi misali da masu kutse da baburan haya zuwa yankunan mahadar Area 1 da AYA a Asokoro. Sai kuma manyan titunan da ake bi wajen shiga ko fita birnin kamar babbar hanyar Kubwa da ta filin jirgin saman Abuja sai kuma wadda ta nufi Nyanya. Ya ce baburan wadanda jami’an tsaro na hadin gwiwa da kotun tafi-da-gidanka ke kamawa, ana kai su wani ofishin hukumarsu da ke Wuye, sannan kotun ke cin tararsu bayan yi musu hukunci sannan a ba su rasidi.

Malam Bodinga ya musanta zargin cewa suna yin gwanjon baburan, inda ya ce  baburan da aka kai dajin Gosa ana lalata su ne tare da kwalmada karafansu don sayarwa ga kamfanonin karfe a kan tsarin sikeli, haka nan robobin da ke jikinsu.