✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta kama hanyar cin La Liga karo na 34

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na dab da lashe gasar La Liga ta Spaniya karo na 34 bayan lallasa kungiyar Getafe a ranar Alhamis.…

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na dab da lashe gasar La Liga ta Spaniya karo na 34 bayan lallasa kungiyar Getafe a ranar Alhamis.

A halin yanzu, Real Madrid wadda ta lashe gasar sau 33 ce take saman teburin gasar da tazarar maki hudu bayan da mai biye mata Barcelona ta yi barin maki hudu a wasanni biyu a jere.

Kafin koma-bayan da ta samu, Barcelona ce take jan zarenta a saman teburin gasar La Liga.

Barcelona ta tashi kunnen doki 2-2 da Celta Vigo kafin kungiyar Atletico Madrid ita ma ta rike ta a wasan da suka buga a makon nan, shi ma aka tashi canjaras ci 2-2.

Hakan ya ba wa Real Madrid damar darewa saman teburin a ranar Alhamis, bayan da ta yi wa kungiyar Getafe ci daya mai ban haushi.

Mai tsaron baya kuma kyaftin na kungiyar, Sergio Ramos ne ya jefa kwallon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.