Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Real Madrid ta sake dauko Zinedine Zidane

Chelsea na zawarcin Zidane
Chelsea na zawarcin Zidane

Zinedine Zidane ya dawo aikin horar da Real Madrid, watanni 10 bayan ya ajiye aikinsa.

Zidane ya maye gurbin Santiago Solari ne wanda ya jagoranci kulob din na kusan tsawon wata biyar.

ADVERTISEMENT

Tsohon dan wasan na Madrid mai shekara 46, ya bar horar da kulob din ne bayan lashe gasar Zakarun Turai sau uku a jere.

Yanzu haka Madrid suna mataki na uku a teburin La Liga, tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona wadda ke saman teburi da maki 63 kamar yadda BBC ta rawaito.

ADVERTISEMENT

Real ta raba gari da Solari bayan nasarar da ta yi wajen doke Real Balladolid a ci 4 da 1 a wasa a wasan makon da ya gabata, wanda kuma ya zo bayan kashin da Madrid ta sha a hannun Ajad ta Netherlands a gasar Zakarun Turai da kuma yadda Barcelona ta fitar da ita Copa del Ray da kuma doke ta a La Liga.