✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta samu Naira biliyan 114 kudin shiga a shekara

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar ya samu kudin shigar da ya kai…

Florentino Perez Shugaban Kulob din MadridA ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayar da sanarwar ya samu kudin shigar da ya kai Naira Biliyhan 114 kwatankwcin Yuro miliyan 520 a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013 watau a tsakanin shekara guda.
Kulob din ya ce ya samu ribar Yuro miliyan 36.9 kwatankwacin Naira biliyan takwas da miliyan100 bayan cire haraji.  Kenan kulob din ya samu karin ribar kashi 54 daga cikin 100 fiye da abin da ya samu a shekarar 2011 zuwa 2012.
Da wannan adadi, kulob din Madrid ya zama zakara a matsayin kulob din da ya taba samu kudin shigar da ya wuce Yuro miliyan 500 a shekaru biyu a jere.
Haka kuma kulob din ya bayyana cewa ya samu damar rage basussukan da ake binsa da kashi 27.4 bisa 100.  A halin yanzu bashin da ake bin kulob din ya tsaya a Yuro miliyan 90 bayan ya samu sukunin biyan yuro miliyan 34.
A ranar 22 ga watan Satumbar da muke ciki ne kulob din zai gabatar da rahoton samun ribar ga Manyan daraktocinsa don sanar da su da kuma neman amincewarsu don ya zama doka.
Idan za a tuna a tarihin cinikin ’yan kwallo babu kulob din da ya kama kafar na Real Madrid.
A watan jiya ne kulob din ya sayi dan wasan gaban  Tottenham da ke Ingila a kan Fam miliyan 88 kwatankwacin Yuro miliyan 100 da hakan ya janyo hankalin daukacin masu sha’awar wasan kwallo a duniya.