Da Dumi Dumi

Rediyo rfi ya cika shekara 12 da kafuwa

A dama Shugaban Sashen Hausa na Rediyo RFI Robert Minangoy ne tare da Babban Edita Bashir Ibrahim Idris a ofishinsu da ke Legas
A dama Shugaban Sashen Hausa na Rediyo RFI Robert Minangoy ne tare da Babban Edita Bashir Ibrahim Idris a ofishinsu da ke Legas

Aminiya: Wace nasara kuka samu a cikin wannan lokaci?

Robert Minangoy: A matsayin Shugaban Sashen Hausa da Suwahili na rfi ina matukar farin ciki a kan irin nasarori da muka samu a cikin wannan takaitaccen lokaci. Da harshen Hausa aka fara amfani a lokacin da aka fara watsa shirye shiryen wannan gidan rediyo. Nasarar da aka samu daga bangaren sashen Hausa ita ce, ta kai ga bude sashen harsuna 3 na Kiswahili da Mandenkan da Fulfulde duka a cikin shekaru 12. Kafin a bude wannan gidan rediyo na rfi akwai dangantaka tsakanin shi da Gidan Rediyon Najeriya BON. Dalili kenan da yasa aka kawo tashar sashen Hausa na rfi zuwa nan babban ofishin BON a Legas kafin mu dawo sabon ofishinmu na yanzu. Gwamnatin Kasar Faransa ita ce take bayar da kudin da ake tafiyar da ayyuka na wannan rediyo. Kuma kasar Najeriya ita ce, kan gaba wajen yawan masu sauraro fiye da miliyan 10 kuma akasarinsu suna sauraron mu ne daga Arewacin kasar a inda babu wadatar wutar lantarki kuma babu na’urorin internet. Suna sauraro ne daga rediyo da wayoyin salula da mutane ke amfani da su a yanzu. Sai kasar Nijar da ke biye da tashoshin Fm a garuruwan Agadas da Tawa da Zindar da Yamai da Marwa da Garwa a Kamaru da rfi take hada mu domin watsa shirye shiryenmu ga masu sauraro.

Sauran kasashen da ke makwabtaka da Najeriya suna kama mu ne a gajeren zango. Saboda ci gaban da rfi ya samu a cikin wannan lokaci yanzu akwai manhaja ta Radio France International da mai sauraro zai iya kama tashar mu a ko’ina a duniya ta wayar salula a lokacin da muke watsa shirye-shirye ko bayan an gama shirin. Dangane da kalubale kuwa, karancin kayan aiki suna taimakawa wajen rage karfi ko tasirin ayyukan da ake yi.

Amma duk da haka akwai kyakkyawan fatan ganin an samu ingantattun kayan aiki da ma’aikata da sake  matsuguni daga Legas zuwa Abuja.”

Babban Edita Bashir Ibrahim Idris yana daga cikin mutanen da suka bayar da gudunmawar kafuwar wannan gidan rediyo rfi tun farko. Ya ce, ”babu abun da zan ce sai godiya ga Allah (SWT) da ya kasance muna daga cikin wadanda suka taka rawa tun farko wajen fara aikin bude wannan gidan rediyo rfi a shekara ta 2007 shekaru 12 da wucewa. A lokacin da muka fara wannan aiki kowa ya sani cewa, akwai wasu kafofin watsa labarai na duniya da suka shafe shekaru fiye da 50 suna aiki da muka zo muka taras da su a wannan fage. Gudunmawar da ma’aikatan da suka fara wannan aiki a wancan lokaci suka bayar ita ce ta kaimu ga karbuwa da hannu biyu inda alkalumma suka nuna cewa akwai masu sauraro fiye da miliyan 10 a Najeriya kadai bayan kasashen Nijar da Kamaru da Chadi da Ghana da Jumhuriyar Benin da sauran kasashen duniya.”

ADVERTISEMENT

Aminiya: Rediyo RFI ta fara watsa shirinta ne cikin wani yanayi na tabarbarewar tsaro a Najeriya. Me za kace a kan haka?

Bashir Ibrahim Idris: A gaskiya a shekara ta 2007 da muka fara aiki ana zaune lafiya a Najeriya. A wancan lokaci matsalar tsagerun Neja-Delta ita ce, kadai babbar matsalar tsaro a Najeriya. Daga baya ne aka samu rikicin ’yan Boko Haram da manoma da makiyaya da masu satar mutane da garkuwa da su da ya bullo daga baya. Kamar yadda aka yi maka bayani tun farko wannan gidan rediyo mallakar gwamnatin kasar Faransa ne ita ta kafa shi ita take bayar da kudaden da ake gudanar da ayyukansa.

Saboda haka babu wani takunkumi na iyakacin abun da za mu iya yin magana a kai da wanda ba za mu iya cewa komai a kansa ba. Wannan ne ya bamu damar tura wakilanmu zuwa kowa ne sako idan wani abu ya auku domin dauko mana labarai da za mu watsa ga masu sauraronmu a duniya. Idan wakilan namu ba sa kusa sai mu buga waya mu tuntubi mutanen da al’amuran ya shafa da hukumomi domin fayyace labaran gaskiya ga masu sauraronmu. Ina daya daga cikin masu bugun kirji da godiya ga Allah a kan cewa, tun da muka fara wannan aiki shekaru 12 da wucewa ko sau daya mahukunta basu taba samun mu da laifin karya ka’idar aiki ba.

Daga karshe, ina shaida maka cewa dukkan bukatar ma’aikatan da ke aiki a wannan gidan rediyo rfi ba ta wuce biyan bukatar mai sauraro ba ta fannin sanin abubuwan da ke faruwa a duniya da sanarwa duniya halin da yake ciki. Kuma muna sanar da masu sauraron mu cewa, su sani fa kofa a bude take wajen karbar koke-koke da shawarwari na halin da suke ciki, musamman a tsakaninsu da jama’a da tsakaninsu da mahukunta, domin aikin namu ke nan na watsa labarai da ilmantarwa  da nishadantarwa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya