✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ribar tarurrukan zuba jari da Buhari ke halarta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana birnin Landan don halartar taron koli kan zuba jari da Birtaniya ta shirya a tsakaninta da kasashen Afirka da nufin…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana birnin Landan don halartar taron koli kan zuba jari da Birtaniya ta shirya a tsakaninta da kasashen Afirka da nufin kulla sababbin yarjeniyoyin kasuwanci domin kara bunkasa tattalin arziki a tsakaninsu.

A wani rahoto na musamman da sashin Hausa na BBC Hausa ya wallafa, ya bayyana cewa, taron wanda shi ne irinsa na farko da Birtaniya, mai neman ficewa daga Tarayyar Turai a karshen watan Janairun da muke ciki ta shirya, ya gayyato gwamnatoci da ’yan kasuwa da cibiyoyin kasashen duniya domin su tallata irin albarkatun da Afirka ke da su.

Sannan su tallata damar da ’yan kasuwa ke da ita ta bunkasa harkokinsu ta hanyar zuba jari da samun riba a nahiyar. Firayi Ministan Birtaniya, Mista Boris Johnson ya yi amfani da wannan dama wajen tallata kasarsa a matsayin wadda ta fi dacewa kasashen Afirka su runguma wajen yin huldar cinikayya, musamman bayan ficewar kasarsa daga Tarayyar Turai. Ana ganin taron a matsayin daya daga cikin matakan da Birtaniya ke dauka masu alaka da ficewarta daga Tarayyar Turai, da zai haifar da sauye-sauye a huldodinta na cinikayya da kasashen duniya.

Taron na Birtaniya ya mayar da hankali ne kan batun cinikayya a tsakanin bangarorin don bunkasa tattalin arzikinsu da tallafa wa ci gabansu da kuma samar da makamashi marar gurbata muhalli.

 

Tafiye-tafiyen Buhari cikin shekara biyar

A baya an gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke cikin shugabannin Afirka 15 da suka samu halartar taron,zuwa ire-iren wadannan tarurruka a wasu manyan kasashe.

A lokacin tarurrukan na baya Shugaba Buhari da gwamnatoci da kuma kamfanonin kasashe sun kulla yarjejeniyoyi da nufin jawo karin masu zuba jari zuwa Najeriya da kuma kawo wa kasarsa ci gaba.

Bayan haka kasar ta kuma dauki wasu karin matakai da suka hada da fito da wasu tsare-tsare a kan hajoji da kamfanoni na ’yan kasashen waje da nufin ba su kwarin gwiwar yin kasuwanci a Najeriya.

Kusan dukkan manyan kasashen duniya sun mika wa Najeriya irin wannan gayyata, kama daga China da Rasha da Jamus da Amurka da kuma Birtaniya a yanzu.

 

Muhimmancin tafiye-tafiyen Buhari

Masu sharhi da masana tattalin arziki na cewa halartar irin wadannan tarurruka na da muhimmanci ga Najeriya. Gayyatar da Shugaban ke samu zuwa tarurrukan na nuna yadda manyan kasashe ke ganin kimar Najeriya da Shugaba Buhari tare da tunanin za su amfana ta hanyar huldar kasuwanci da Najeriya.

Ta fannin diflomasiya kuma, shugabanni masu kima ne manyan kasashe ke gayyata domin su tattauna. Bayan haka halartar tarurrukan da Shugaban Kasar ke yi za ta taimaka wajen tallata kasar nan a idon duniya.

 

Ribar da Najeriya ta samu

’Yan Najeriya sun sha bamban kan yadda suke ganin tasiri ko ribar da kasar ta samu daga irin wannan ziyarar da ake gayyatar Shugaban Kasar.

Daga cikinsu akwai masu korafin cewa har yanzu ba a aiwatar da akasarin yarjejeniyoyin da Shugaban Kasar ya kulla da kasashen ba a lokacin irin wadannan ziyara.

Daga cikin akwai wadanda suka kosa cewa har yanzu ba a fara aiwatar da yarjejeniyar samar da wutar lantarki da kasar ta kulla da Jamus yadda ya kamata ba.

A fahimtarsu yarjejeniyar wutar lantarkin na cikin wadanda kasar za ta fi amfana da su idan aka aiwatar da ita kamar yadda aka kulla.

Suna kuma nuni da cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da China kan amfani da kudaden kasar China maimakon Dalar Amurka a wajen huldar cinikayya ba.

Kazalika ’yan China ba su zo sun kafa kamfanoni a kasar nan kamar yadda aka yi alkawari ba.

Amma kuma wadansu ’yan Najeriya na ganin cewa yarjejeniyar samar da takin zamani da kasar ta kulla da Moroko ta biya bukata, domin a cewarsu sun gani a kasa, inji Farfesa Garba Ibrahim Sheka, masanin tattalin arziki.

Farfesa Sheka ya bayyana cewa akwai alamun batun aiwatar da yarjejeniyar wutar lantarkin za ta taso nan ba da jimawa ba idan aka yi la’akari da yadda gwamanti ke magana kan batun a baya-bayan nan.

A cewarsa, yawancin manyan kasashen da ke neman kulla alakar cinikayya da kasashen Afirka na yin haka ne domin samun ciniki idan aka yi la’akari da yawan mutanen nahiyar.

“Bayan haka ’yan kasuwa da ke halartar irin wadannan tarurruka kan samu riba ta yadda suke samun damar kulla huldar kasuwanci a kasashen.

‘Kasashen da ke gayyatar Najeriya na da manufofinsu da kuma bukatun da suke neman cimmawa daga kasashe masu tasowa irin Najeriya.

“Don haka sun fi mayar da hankali wurin cika alkawuran da suka ga bukatunsu za su biya.

“A wani lokaci kuma yarjejeniyoyin na tattare da wasu sharudda ko ka’idoji masu wuyar cikawa, wadanda a sakamakon haka ba a iya aiwatar da su yadda aka tsara,” inji shi.

Farfesa Sheka ya ce yawanci in ban da China wadda kan bayar da kudaden da ta yi alkawari da sauransu, abin da sauran kasashen ke ba wa kasashe masu tasowa bai wuce lamuni ko bashi ba.

Ya ce, “Duk da haka kasashen ba su fiye zuwa Afirka domin bude kamfanoni da masana’atu domin samar da ayyuka yadda kasashen nahiyar ke bukata ba.” A cewar rahoton na BBC

 

Ina matsalar take?

Gaskiyar magana ita ce duk kasashen da ke neman kulla alaka da Najeriya ko sauran kasashen Afirka, makasudinsu shi ne samun riba ta kai-tsaye ko a kaikaice.

Don haka kasashe masu neman a kulla irin wannan alaka kan ayyana bukatun da suke neman cimmawa gwargwadon manufofin kasashensu da kuma matakan aiwatar da su tun kafin su kira taro.

Su ke da cikakkiyar sani da shiri game da abin da taron ya kunsa da yadda za su bijiro da abin da suke bukata ga mahalarta.

Akasari masu masaukin baki ne ke tsara yarjejeniyoyin da sharudda da kuma ka’idojinsu sannan su gabatar wa baki a lokacin tattaunawa domin rattaba hannu.

Ana iya cewa mahalarta taron ba su da wadataccen lokacin yin nazari mai zurfi da ma tuntubar juna a cikin kurarren lokacin.

Duk da cewa a wasu lokutan kasashe masu tasowa kan gabatar da nasu bukatun, masana na ganin bukatunsu sun fi karkata ne a neman tallafi.

Bayan haka manyan kasashen ke da wuka da nama domin sun fi bayar da kaso mai yawa na kudaden na hadin gwiwa da ake bayarwa domin ci gaba a kasashe irin Najeriya.

Shi ya sa yawanci ake ganin tamkar kasashe masu tasowar kan halarci irin wadannan tattaunawa ne dauke da kokon bara, inji Farfesa Sheka.

A wasu lokuta kuma kasashe irin Najeriya ba su cika nasu bangaren alkawarin da zai ba wa Turawa kwarin gwiwar cika nasu bangaren ba.

Akwai kuma yiwuwar manyan kasashen su ki mayar da hankali a kan duk huldar da suka ga ba za su samu ribar da suka yi tsammani ba a kai.

Bugu da kari kasashe irin Najeriya ba su da karfi ta fuskar masana’antu da sarrafa albarkatun kasashensu ta yadda za su iya kwadaita wa manyan kasashe su shigo cikin natsuwa.

Kazalika ci gaba ta fuskar fasahar zamani wanda shi ne babban abin da duniya ke bukata a yanzu na da karanci a kasashen Afirka idan aka kwatanta su da takwarorinsu.

Ya ce saboda haka akwai yiwuwar manyan kasashen ne za su fi cin moriyar irin wannan alaka lura da yadda kasuwancin zamani ke tafiya.

Za su ci gaba da shigo da kayayyakin da suka sarrafa a kasashensu, koda kuwa daga Najeriya aka samu kayan da ake bukata domin haka.

 

Kasuwar hannun jari

Rahoton da kasuwar hada-hadar hannun jari ta Najeriya ta fitar a baya-bayan nan ya ce ’yan kasashen waje sun janye hannun jarin Naira biliyan 491 daga kasuwar a tsakanin Janairu zuwa Nuwamban bara.

Rahoton ya ce adadin hannayen jarin da ’yan kasashen waje suka janye ya haura kashi 20.4 cikin 100 na adadin da suka janye a bara.

Farfesa Sheka ya ce hakan na da ban mamaki ganin cewa babu wata babbar barazanar tsaro a fili a kasar nan.

“Baya ga zuba jari domin samun riba kai-tsaye, ’yan kasuwa kan zuba jari domin cin riba daga darajar kudin kasashen da suka zuba jari.

“Neman daidaita farashin Naira da Najeriya ke yi na iya kasancewa dalilin da ya jawo janyewar ’yan kasuwar.

“Irin wadannan ’yan kasuwa kan sayi hannun jari a kasashen da darajar kudinsu ta fadi, ta yadda cikin dan lokaci kudin za su samu riba mai yawa.

“Yanayin tattalin arzikin kasashensu na iya zama dalilin mayar da kudadensu gida.

“A yayin da mutane ke fitar da dukiyoyinsu daga kasashensu zuwa wasu kasashe domin samun riba, rashin samun riba fiye da na kasashensu na iya sa su mayar da kudadensu gida.

“Bayan haka tafiyar hawainiya da tattalin arzikin wasu kasashen Turai ke fama da shi kan sa wadansu ’yan kasashen waje mayar da kudadensu gida domin kishin kasa da zimmar taimaka wa wajen farfado da tattalin arzikin kasashensu,” inji Farfesa Sheka masanin tattalin arzikin.

 

Mene ne abin yi?

Ga jerin matakan da masana tattalin arziki suka ce ya kamata kasar ta bi:

i. Sun nuna bukatar kasar ta bibiyi yarjeniyoyin da ta kulla a irin wadannan tarurruka ko gayyata da aka yi mata domin tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata.

ii. Sannan wajibi ne Najeriya  ta tabbata tana cika nata bangaren alkawarin ko ka’idoji da sharuddan da yarjeniyoyion suka kunsa.

iii. Ya kamata Najeriya ta inganta albarkatunta yadda ya kamata ta yadda za ta iya tallata su ga kasashen a yayin kulla wasu yarjejeniyoyin.

ib. Akwai kuma bukatar Najeriya ta rika yi wa alkawuran nazari mai zurfi domin fahimtar irin abin da suka kunsa da irin tasirin da za su yi da ma yiwuwar aiwatar da su.

b. Tun kafin halartar irin wadannan zama akwai bukatar Najeriya ta samu kyakkyawar fahimtar abin da taron ya kunsa da abin da za a bukata daga gare ta sannan ta dauki matsayi tun kafin lokacin.

bi. Kafin ta rattabata hannu, yana da muhimmanci Najeriya ta tabbatar cewa a shirye take kuma za ta samu moriya ta zahiri a yarjeniyoyin yadda ya kamata.

iib Najeriya ta kasance ita ma tana gindaya sharudda tare da mika bukatun da suka dace da yanayinta ba wai sai abin da aka yi mata tayi ba.

iiib Yana da kyau Najeriya ta guji yin gaggawa sannan ta yi kyakkaywan shiri da fahimta kafin ta shiga irin wadannan yarjejeniyoyi.