Da Dumi Dumi

Ribery, Ronaldo da Messi ne za su fafata a Gwarzon dan kwallon Nahiyar Turai

Frank Ribery , Cristiano Ronaldo da Lionel MessiA shekaranjiya Laraba ne hukumar shirya wasan kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta fitar da jerin sunayen  fitattun ’yan kwallo a Nahiyar Turai da ake kyautata zaton daya daga cikinsu ne zai kasance gwarzon dan kwallon Nahiyar Turai.
Zaben zai gudana ne a ranar Alhamis 29 ga watan nan da muke ciki a Monaco da ke Faransa ranar da ake sa ran fitar da jadawalin gasar cin kofin Nahiyar Turai da aka fi sani da UEFA Champions League.
’Yan kwallon da za su fafata a tsakaninsu sun hada da Frank Ribery, da ke wasa a kulob din Bayern Munich da ke Jamus, kuma an zabe shi ne saboda namijin kokarin da ya yi a kakar wasan da ta wuce bayan ya taimaka wa kulob din Bayern lashe manyan kofuna uku da suka hada da kofin zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai (UEFA Champions League) da kofin gasar rukuni na Jamus (Bundesliga) da kuma kofin kalubale a Jamus.
Sannan an zabi Cristiano Ronaldo da ke wasa a kulob din Real Madrid da ke Sifen ne saboda taimaka wa kulob dinsa wajen zura kwallaye 12 a raga a gasar zakarun kulob-kulob na Turai kuma ya zama dan kwallon da ya fi kowane zura kwallo a lokacin gasar.
Haka kuma an zabi Lionel Messi dan kwallon FC Barcelona ne saboda taimaka wa kulob  dinsa wajen zura kwallaye 46 a raga a gasar rukuni-rukuni ta Sifen da aka fi sani da La-Liga a kakar wasan da ta wuce da hakan ta sa kulob dinsa lashe kofin La-Liga a kakar wasan da ta wuce.
An zabo wadannan ’yan wasa uku ne daga cikin 10 da hukumar ta tantance tun da farko a kwanakin baya.
’Yan jaridu da suka fito daga daukacin Nahiyar Turai da ke karkashin Hukumar kula da wasan kwallo ta Nahiyar Turai (UEFA) ne ake sa ran za su gudanar da zaben.  Hukumar ta ce, za a nuna zaben kai tsaye a akwatunan talabijin inda ake sa ran daukacin jama’a za su iya kalla a ko’ina suke a duniya.  Sannan nan take ake sa ran bayyana wanda ya lashe zaben.
A shekarar 2011 ce aka fara gudanar da wannan gasa a tsakanin ’yan kwallon Nahiyar Turai.
Lionel Messi ne ya fara lasheta a shekarar 2011 yayin da takwaransa Andre Iniesta ya lashe a shekarar 2012.  Sai dai Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ne ’yan kwallon da sunayensu suke cikin wadanda suke fafatawa a duk shekara tun lokacin da aka bullo da gasar.

Share