✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Riga da wando na talauci a Arewa

Tun kafin zuwan Turawa ake ta gwagwarmayar yaki da talauci a yankin Arewacin kasar nan amma har yanzu ba a kai ga nasara ba, domin…

Tun kafin zuwan Turawa ake ta gwagwarmayar yaki da talauci a yankin Arewacin kasar nan amma har yanzu ba a kai ga nasara ba, domin kullum talakawa sai karuwa suke yi kamar farin dango.

Hakan na faruwa ne saboda al’ada da kuma wasu abubuwa da suke faruwa a yankin wadanda suke bai wa dashen talaucin da aka dasa ruwa. Shi ya sanya tun a zamanin Turawa aka samu wadansu bayin Allah da suka himmatu suna yaki da zalunci da lalaci da talauci a yankin Arewa.

Talauci ya rika yaduwa a yankin Arewa saboda al’ada, inda za ka ga mutum guda yana daukar nauyin mutane da yawa shi kadai, shi ne cinsu da shansu da suturarsu da wurin kwanansu, ba su da aikin komai sun zauna ne kawai suna jiransa ya nemo ya kawo musu, ba za su tashi su nemi nasu ba saboda ‘namu ya samu.’ Saboda mutuwar zuciya ne ya sanya a yankin Arewa za ka ji ana cewa ‘ Allah Ya ba ku mu samu,’ maimakon a rika cewa ‘Allah Ka ba mu namu.’

Za a iya ganin yadda al’ada ta yi tasiri wajen kashe zuciyar mutane a yankin Arewa idan aka saurari wakar da marigayi Mamman Shata ya yi lokacin da aka nada marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, inda Shata yake fadi a wakarsa cewa Sarki Ado ya je ya durkusa a gaban Sarki Sanusi da aka sauke ya ce masa daga yanzu shi ne zai rika daukar dawainiyar mutanen da yake ciyar da su da tufatar da su da yi musu aure da saya musu ragon suna da sauransu da yawa. Ya ce masa ‘Wadannan bar ni da su na ba su.’

Wannan ya nuna irin yadda a kasar Hausa mutane ke zaunawa suna jiran dan uwansu ko ubangidansu ya rika yi musu komai ba za su tashi su nemi nasu ba, saboda namu ya samu. A Jamhuriyya ta Biyu na ga wani bawan Allah  da ya je aiki a ‘Railway’ a matsayin direba sai abokinsa ya ci zabe ya zama dan Majalisar Tarayya, tun kafin a rantsar da su wannan direban ya ajiye aikinsa saboda wai ba zai yi tuki ba tunda yanzu ‘namu ya samu!’

Haka nan mutane suke zaune da matacciyar zuciya ba su so su tashi su nemi nasu sai dai su rungume hannu suna jiran dan uwansu da yake da kokarin nema shi ne zai rika yi musu komai,  idan kuma nauyi ya yi masa yawa ya kasa a rika zaginsa.

Babu shakka taimaka wa ’yan uwa abu ne mai kyau kwarai, amma bai kamata don mutum yana da mai taimaka masa ya yi zaune ya shantake ya ki tashi ya nemi nasa ba.

Bayan al’ada yanzu kuma matsalar tsaro ta taimaka wajen talauta mutanen yankin Arewa, domin muhimman hanyoyin neman dukiya a yankin su ne noma da kiwo da fatauci, yanzu duk an takura wa masu yin su, babu damar zuwa gona sai masu garkuwa da mutane su kama mutum sai an biya kudi a sake shi, idan kuma ba a yi sa’a ba a kashe shi, kamar yadda wadansu mugaye suka kashe wadansu manoma a gonakinsu a yankin Batsari a Jihar Katsina saboda sun je noma abin da za su ci. Wadannan mugayen mutane sun same su suka ce musu ‘ba mun ce kada wani ya yi noma ba,’ sai suka bude musu wuta suka kashe su. Saboda haka yanzu mutane suna jin tsoron zuwa gonakinsu.

Tunda farko da satar shanu aka fara, inda za a kora shanun mutum gaba daya a tafi da su, idan ya nemi yin jayayya a kashe shi. Daga nan sai suka koma sace mutane tunda sun ga ya fi satar shanu sauki da samun kudi. Wadansu daga cikinsu saboda an sace musu shanunsu an gurgunta su ne suka kasa daurewa suka zama masu garkuwa da mutane.

Saboda haka suke tare hanyoyi suna kama matafiya da suke zirga-zirga a kan hanyoyi domin neman halaliyarsu, sai a rike su a sanya makudan kudi da za a biya kafin a sake su, wadanda ba su da kudin biya sai an sayar da komai nasu da na ’yan uwa kafin a hada kudin, wani kuma ko an biya kudin ba za a sako shi ba sai a kashe shi.

A irin wannan halin ne yanzu ake zaune, an hana noma an hana kiwo an kuma hana fatauci, ta yaya arziki zai yadu har mutane su amfana? Wanda yake da shi an gurgunta shi ya koma bai da shi, mai kokarin nema an tsorata shi, sannan ba a so a yi noma, ta yaya za a zauna lafiya?

Ya kamata masu garkuwa da mutanen nan su fahimci cewa idan ba su bari an yi noma an yi fatauci ba, su ma babu abin da za su yi da takardun kudin da suka kwace, domin ta wadannan hanyoyin ne za su samu abincin da za su saya da kudin da kuma samun sauran muhimman kayayyakin rayuwa.

A halin yanzu sai jaruman gaske suke iya zuwa gona, manyan manoma da dama sun hakura da gonakinsu. Wanda hakan ya sanya talakawa masu kwadago suke rasa aikin yi.

Idan aka lura za a ga cewa an yi wa al’ummar yankin Arewa dabaibayi ta fuskar neman arziki, shi ya sanya harkoki suka tsaya, kowa yana kuka, ana cewa babu kudi, talauci ya yi kanta. Ga marayu da zawarawa a kullum sai karuwa suke yi saboda an kashe mazansu.

Saboda haka duk wani kokari da gwamnati za ta yi domin yaki da talauci zai zama a banza matukar babu tsaro, domin idan babu walwala babu yadda za a iya neman arziki tunda sai da rai da lafiya ake yin komai.