Search
Subscribe
Rigakafin cututtuka don maniyyata

Rigakafin cututtuka don maniyyata

Dangane da masu niyyar sauke farali, shin akwai wasu abubuwa ne na lafiya da ya kamata su kiyaye kamar tafiya da wasu magunguna na wasu cututtuka da hanyoyin da za a kiyaye su?

Amsa: Eh, kwarai kuwa, aikin Hajji na daya daga cikin lokutan da akan bukaci maniyyata su dauki matakan kariya daga wasu cututtuka. Kuma an yi bayanin haka a shekarun baya. Duk hukumomin lafiya da na jin dadin alhazai sukan tanadi wannan. Akwai cututtuka aji biyu wadanda ake yi wa allurar rigakafi; cututtukan da maniyyaci zai kwasa ya tafi da su aikin Hajji da kuma wadanda zai iya kwasa a can. Dukkansu ana bukatar maniyyaci ya kiyaye kansa daga su. Mutum miliyan uku zuwa hudu daga kasashe kusan 200 ake sa rai su halarci wannan ibada. To a likitance duk inda za a samu taron jama’a na dubbai ma ana so a yi taka-tsantsan ballantana taron miliyoyi. Don haka ne ma Hukumar Kiyaye Cututtuka ta Duniya (CDC) ta fitar da tsarin rigakafin kiyaye cututtuka masu yaduwa a irin wadannan lokuta, wadanda ya kamata kowane maniyyaci ya karba.

A tsarin hukumar dole ne idan ana so a je lafiya a yi ibada lafiya a dawo lafiya sai an karbi allurar rigakafin cututtukan da akan samu a garin maniyyaci kamar ciwon sankarau da na shawara wato Yellow feber da sauransu. Wato dai duk wasu allurai da magungunan rigakafin cututtukan da suka yi kamari a garin maniyyaci, kamata ya yi a ce ya karbe su. A nan kasarmu ban da ciwon sankarau da na shawara, mukan yawaita samun ciwon zazzabin cizon sauro da na taifot, don haka dole ne maniyyaci ya je ya karbi magungunan kariya daga maleriya (kamar maganin Fansidar) da kuma allurar rigakafin taifot (typhoid baccine) da allurar rigakafin shawara (yellow feber baccine) da ta sankarau (meningitis baccine). Sai kuma a cewar hukumar, yana da kyau mutum ya kare kansa daga cututtukan da zai iya tararwa a can, kamar ciwon mura (inda zai karbi allurar rigakafin mura (influenza baccine) da ciwon hanta nau’in A (inda ya kamata ya karbi allurar rigakafin hepatitis A baccine domin kariya).

Hukumomin kasar da ake aikin Hajjin su ma suna da nasu tsarin tabbatar da cewa maniyyata sun karbi rigakafin da ya kamata domin ganin an kare mahajjata daga kamuwa da cututtuka. Sukan bukaci katin shaidar cewa an yi wa maniyyaci alluran a wasu lokuta. A wasu lokuta ma su sukan bayar da kansu. Domin idan aka lura a ’yan shekarun nan maniyyata daga kasa kamar tamu da an sauke su a filin jirgi ake ba su digon bakin rigakafin ciwon shan-inna da wasu kwayoyin magani na kiyaye mura da ciwon sanyin kirji. Wadansu sun ce saboda ba su yarda da takardun shaidar da maniyyatanmu sukan nuna ba ne, tunda wasu takardun kamar kati mai launin ruwan dorawa a filin jirgi ake saya ba tare da an yi allurar ba.

Haka nan Hukumar Hajji ta Kasa a shafinta na Intanet ta wallafa cewa dole kowane maniyyaci ya karbi alluransa na rigakafi tun daga gida Najeriya, a cibiyoyin da hukumomin jihohinsu suka ware, ko ya tuntubi kamfanoni masu jigilar alhazai idan a jirgin yawo zai je. Maniyyaci ya kuma tabbatar an ba shi takarda ko katin shaida domin adanawa.

To wannan a bangaren allurai da magungunan rigakafi ke nan. A daya hannun kuma akwai maniyyata masu wasu cututtuka na tsawon lokuta kamar hawan jini, ciwon suga, ciwon sanyin kashi, farfadiya, ciwon asma da sauransu. Su ma masu wadannan matsaloli dole su kula su taho da magungunansu idan an zo tashi, kada su manta, kuma yana da kyau su karbi takardar asibiti mai sa-hannun likita cewa su wadannan magunguna na cututtuka kaza ne suke sha, ba na safara ba, domin kada a kwace a filin jirgi. Duk da cewa akan samu asibitoci da kananan wuraren shan magani kyauta a ko’ina a wuraren aikin Hajji, dole mai wani ciwo ya rike irin maganin da yake sha a gida da takardun sa-hannu na likita domin koda sun kare a kara masa wasu a can.

Sa’annan ban da wadancan cututtuka na tsawon lokuta, akwai kanana wadanda ake so mahajjata su kiyaye, irin su amai da gudawa, bugun rana, dimuwa, ciwon jiki da sauransu. Hanyoyin kariya daga wadannan matsaloli sun hada da:

  1. Domin kiyaye cututtukan gudawa akan so a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin cin abinci da bayan shiga bayi. Haka nan tabbatar da tsabtar abinci da ruwan sha shi ma yakan rage samun wannan matsala. A rika lura sosai da abinci musamman a wurin wadanda sukan dafo a gida su kawo titi wanda zai iya yada amai da gudawa. Za a iya cin irin abincin idan a cikin gida aka dafa a gaban Alhaji kuma a cikin gida aka sayar, wato ba wanda aka kawo kan titi ba. Domin wasu lokuta ire-iren abincin da muka saba ci sai an shiga gidajen mutanenmu mazauna can akan samu.
  2. Domin kiyaye bugun rana dole a kiyayi shiga rana, wato a kiyayi fita tsakar rana, ko a rika yawan amfani da lema saboda bana ma lokacin zafi da rana za a yi aikin
  3. Domin kiyaye dimuwa dole mahajjata su rika yawo da katin shaida, kuma a cikin ’yan uwa kada wani ya zame ya bata, domin sau da dama da mutum ya bata yake dimaucewa saboda bakunta
  4. Domin kiyaye ciwon jiki kada mutum ya gajiyar da kansa da tafiyar kafa da yawa. Idan za a je wuri mai nisa a shiga mota duk da cewa kamar akwai tsada, idan za a dawo sai a tako idan an gane hanya.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin