Da Dumi Dumi

Rikcin Nasarawa: Za mu tafi Kotun daukaka kara –Lauyan Ombatse

Barista Zachari Zamani AlumagaA kwanakin baya ne lauyoyin kungiyar Ombatse da ake zargi da kashe jami’an tsaro sama da 100 a Jihar Nasarawa suka janye daga zaman Kwamitin Binciken Rikicin da ke zama a Lafiya. Wakilinmu ya tattauna da Babban Lauyan Ombatse Barista Zachari Zamani Alumaga wanda shi ma dan kabilar Eggon ne game da dalilin janyewansu da kuma batutuwan da suka shafi rigirgimun kabilanci a jihar:

Aminiya: Barista me ya sa kuka janye daga zaman Kwamitin Binciken Kisan Jami’an Tsaro da aka yi a Alakio bayan an soma da ku?
Alumaga: kwarai da gaske mun janye, dukanmu lauyoyin kungiyar Ombatse mun zauna mun tattauna a kan wasu abubuwa kafin mu tafi gaban kwamitin inda ake gabatar da korafi. Muna da wasu kudurori; na farko shi ne mu je gaban kwamiin ne don mu tabbatar musu da hadin kanmu sannan daga baya mu kama gabanmu. Na biyu shi ne mu je a soma gabatar da korafi da mu mu gabatar da namu, sannan mu ci gaba idan muka ga alamun kwamitin binciken ba zai yi magudi ba, domin duniya ta san gaskiyar lamarin. Hakan ya sa muka yi shiri sosai game da wannan zama don a wannan lokaci muna ganin cewa za a nuna gaskiya. Mun so mu yi amfani da wannan damar mu gaya wa duniya namu labarin, mu kuma bayyana sunan wadanda ke hura wutar rigirgimun kabilanci a jihar nan don a san su. Amma da kwamitin ya fara gudanar da aikinsa sai muka lura cewa yana nuna son kai ga wasu kabilu yana nuna kiyayya ga wasu kabilun.
Aminiya: Me kake nufi da kwamitin na nuna son kai ga wasu kabilu da kuma kin wasu?
Alumaga: Ka ga na farko shi ne sashi na 4 a dokar Final Kod na jihar nan wadda ita ce dokar da ta haramta harkokin kungiyar Ombatse, na shawarci shugaban kwamitin binciken ya bincika wasu abubuwa a cikin dokar kafin a ci gaba da zaman. Misali ko wannan doka tana nan tunda ko a ’yan kwanakin nan ne aka kirkiro ta. Ka ga gwamnati tana zargin cewa kungiyar Ombatse kungiya ce ta mayaka. Amma ina so in shaida maka cewa mu ba mayaka ba ne, kuma abin da mu lauyoyin kungiyar muka ki amincewa ke nan. Kai da ake ce ka san mayakan Ombatse ka fito ka bayyana wa duniya sunan wadannan mayaka. Gwamnati ta ce ’yan kungiyar Ombatse ne suka kashe wadannan jami’an tsaro da aka turo kauyen Lakyo. Mun amince cewa wadannan jami’an tsaro an kashe su amma ya kamata kwamitin ya yi adalci ya binciko su wane ne suka kashe su, kuma don me aka kashe su? Dukansu mutane ne kamar kowa, mun san kowa na da nasa ajali, amma ba ajali ne ya rutsa da su ba.
Aminiya: Kana nufin ba ’yan kungiyar Ombatse ne suka halaka wadannan jami’an tsaro ba ke nan?
Alumaga: Abin da nake nufi shi ne gwammati tana zargin kungiyar mayakan Ombatse da aikata wannan danyen aiki. Ni ban san kungiyar mayakan Ombatse ba. Ban tsaya mata ba, na tsaya wa kungiyar Ombatse ne, inda nake ke nan.
Aminiya: Kana ganin don me aka yi wa jami’an tsaron kwanton bauna aka kashe su a kauyen?
Alumaga: A gaskiya ni kaina ina mamakin aukuwar lamarin wanda kamar aikin asiri ne don jami’an tsaron ba su je gidan wani sun kama shi ba. Ba su kuma tafi gonar kowa ba. Da ni da ku ’yan jarida da muka ziyarci kauyen, mun gano lamarin ya auku ne a kan hanya. Saboda haka ba zan iya cewa ga dalilin da ya sa aka kashe jami’an tsaron ba.
Aminiya: Me ka sani game da wata ’yar Fulani budurwa da ake zargi cewa ’yan kungiyar Ombatse sun kashe ta a kwanakin baya?
Alumaga: Ni ma na karanta labarin a wata jarida cewa wani ya kawo wata ’yar Fulani budurwa don ta jagoranci mayakan Fulani su je su yaki mutanen Eggon da ke yankin B.A.D da Rutu da kuma Bassa. Sai dai an kashe ta a kauyen B.A.D an kuma binne wata kwarya da ta dauko a kanta kuma na ji cewa wannan kwaryar Sarkin Ebiera ne ya ba ta don a lokacin ya yi ta yunkurin zuwa kauyen Lakyo don ya kwace kwaryarsa. Haka kuma na ji a labarin cewa an kai kanta kauyen Lakyo. Abin da na karanta a labarin ke nan. Ban san gaskiyar lamarin ba. Tunda nake tafiya Lakyo ban taba ganin inda kan ’yan Fulanin da kwaryar suke ba. Amma idan sun ce sun san inda suke, to, sai su je su kawo su nuna a matsayin shaida.
Aminiya: Yanzu da kuka janye daga zaman kwamitin, wane shiri kuke yi game da lamarin?
Alumaga: Ba za mu so mu bayyana shirin da muke yi yanzu ba, don akwai dabaru da yawa da ake amfani da su wajen kamun birai. Tunda gwamnati tana da damar kafa kwamitin bincike mu ma muna da damar tafiya Kotun daukaka kara. Abin da muke tunanin yi ke nan.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya