Daily Trust Aminiya - Rikice-rikice da ke faruwa a Arewa laifin ’yan siyasa ne -Fa
Subscribe

Rikice-rikice da ke faruwa a Arewa laifin ’yan siyasa ne -Farfesa Ango Abdullahi

Farfesa Ango AbdullahiFarfesa Ango Abdullahi daya ne daga shugabannin kungiyar Dattawan Arewa. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi kasa, musamman yankin Arewa. Ga yadda ganawar ta kasance:

Wasu mutane na ganin cewa kungiyar Kare Muradin Arewa (ACF) ba ta tafiyar da aikinta yadda ya kamata, idan aka yi la’akari da yadda takwarorinta da ke sauran sassan kasar nan ke yi. Ko ma za ka ce ya janyo hakan?
Bari in soma da cewa wannan zance da ake yi cewa wai ACF ba ta komai, ba gaskiya ba ne, musamman kamar yadda ka kawo misali da yadda sauran takwarorinta ke yi a kasar nan. A nan Arewa, muna da wata al’ada da wasu lokuta ake dauka kamar kasawa ko kuma rauni ne saboda kawai mu ba ma fitowa muna zage-zage da sauransu. Wannan ya sanya wasu ke daukar cewa ba mu damu da muradinmu ba, wanda kuma ba gaskiya ba ne.
Dukkanmu ’yan kungiyar ACF ne kuma idan ka yi la’akari da tarihi da tsarin gudanar da mulkinmu, ya banbanta mu da sauran amma ina tabbatar maka da cewa ACF da sauran kungiyoyin kare muradun Arewa a shirye suke su kare hakkokin Arewa kuma a shirye muke mu ga cewa shugabanci ya komo yankin Arewa a 2015. Ina kuma ba ka wannan tabbaci ne a madadin sauran kungiyoyi biyar da ke tare da ACF a yanzu.
Wannan ba kuma yana nuna cewa ’yan Arewa na kwadayin mulki ba ne, domin idan aka yi la’akari da yawan al’umma da kuma cewa zabe na gaskiya za a yi Arewa na da yawan da za ta ci gaba da cin zabe a kasar nan. Amma saboda la’akari da son ganin an zauna lafiya a kasar nan, wasu daga cikinmu da suka zauna aka sake kundin tsarin mulki da siyasar kasar nan a 1987, mun amince da cewa akwai bukatar a fito da tsarin karba-karba a tsakanin bangarorin kasar nan, musamman Arewaci da Kudanci.
Kuma jam’iyar PDP ta amince da wannan tsari domin ina cikin wadanda suka dan yi garanbawul ga tsarin mulki na jam’iyar, cewa akwai bukatar a rika karba-karba tsakanin Arewa da Kudu, musamman dangane da shugabancin kasa. A lokacin nan sai da aka yi ’yar jayayya a kan cewa idan har za a fara karba-karba daga wani yanki za a fara?
Bayan an yi ta ja sai mu ’yan Arewa kamar kullum muka amince da cewa tunda idan aka dubi shugabannin kasar nan na soja da na farar hula da suka shude, duk ’yan Arewa ne. Don haka sai muka amince da cewa a fara karba-karbar daga Kudanci. Ka ji yadda aka yi Obasanjo ya zama Shugaban kasa. Kuma mun amince ne a kan cewa shekaru hudu kacal zai yi. Amma sai daga baya ya roki da a ba shi dama ya kara shekaru hudu domin ya yi daidai da tsarin mulkin kasa da ya ce shugaba na da damar mulkin kasar nan na tsawon shekaru takwas.
Muka amince da hakan kuma Obasanjo shi ne na farko wajen sanya hannu a yarjejeniyar da aka yi, sannan Shugaba Jonathan na wajen a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa. Kuma shi ya sanya hannu a matsayin mutum na 37. Dukkanmu muka amince kudu za ta yi shekaru takwas daga nan sai Arewa ita ma ta yi takwas. Amma daga baya sai Obasanjo bayan ya ji dadin mulki sai ya nemi ya zarce. Da ya ga bukatarsa ba za ta biya ba sai ya sake dawowa Arewa, inda ya dau magajinsa, wato marigayi Umaru ’Yar’aduwa.
Arewa ta sake samun mulki amma dai Umaru ’Yar’aduwa na fama da rashin lafiya kuma ya rasu ne bayan shekaru biyu da rabi a kan karagar mulki. Sannan kundin tsarin mulki ya nuna mataimaki ne zai hau mulki kuma haka aka yi har Goodluck Jonathan ya zama Shugaban kasa. Mu kuma sai muke ganin cewa ko ba komai dai akwai bukatar a bar Arewa ta kammala shekarunta takwas. A 2011 na dauka idan har akwai yarda da sanin ya kamata, Arewa ne ya kamata ta fitar da Shugaban kasa, musamman tunda an san da akwai wannan yarjejeniya ta karba-karba. Wanda kuma duk sun sanya hannu a kai amma sai suka fito fili bainar jama’a suka karyata wannan yarjejeniya. Obasanjo ne ya fara karyatawa, sannan daga bisani shi ma Jonathan ya ce bai san da wannan yarjejeniya ba. Haka kuma daga baya mun samu labarin daga bakin Gwamnan Jihar Neja, cewa gwamnoni ma sun yi irin wannan yarjejeniya da Goodluck, a kan cewa sun yardar masa ne kawai ya yi shekaru hudu amma Shugaba Jonathan ya sake karyatawa.
Wannan irin hali ke nuna ta yaya za a amince wa shugabanni, idan har su da kansu ba su cika alkawura na baki ko na rubuce ba. Cika alkawari alama ce ta shugabanci na gaskiya. Saboda rashin cika mana alkawari da aka yi ne ya sa Arewa ke cewa dole sai mulki ya dawo hannunta kodai ta hanyar karba-karba ko kuma ta hanyar zabe.
Kan wannan zance na karba-karba, ke nan kana nufin tsohon Shugaba Obasanjo ya yaudari ’yan Arewa ke nan saboda haka dole mulki ya dawo Arewa a 2015?
Wannan shi ne abin da muke cewa, ma’ana muna son karbo abin da muke ganin hakkinmu ne a yanzu. Game da zancen ko Obasanjo ya yaudari Arewa, ai shi ya dade yana yaudarar kansa da sauran mutane.
Ka nanata bukatar mulki ya komo Arewa kuma alhalin Arewar nan kan al’ummarta ba a hade yake ba. Ko kana ganin Arewa za ta hade wajen neman biyan wannan bukata?
Wannan tambaya ta hadin kan ’yan Arewa abu ne da muke ta kokarin yi, wato kungiyar ACF da ta Dattawan Arewa da sauran ire-irensu, ba dare ba rana a kasar nan. Zan tabbatar maka cewa dukkanmu babu abin da ke a gabanmu kamar kashe wutar rabuwar kawuna da ke a yankin Arewacin kasar nan, wanda wasu daga waje ke hurawa. Akasarin rikice-rikicen da ke faruwa a Arewa, ’yan siyasa ne kawai ke kawo su saboda biyan bukatun kansu. Amma muna nan muna kokarin magance matsalar kuma da zaran mun magance ta, komai zai daidaita a yankin. Daga nan ne siyasar kasar nan za ta canza, domin sai mun duba inda za mu saka kuri’armu kafin mu jefa.

texem
More Stories