✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikice-rikice: ’Yan siyasa ku yi koyi da magabata – Jalo Daudu

Wani tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya, Dokta Ibrahim Jalo Daudu, ya  ga ’yan siyasar kasar nan cewa su yi koyi da magabatansu…

Wani tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Sadarwa ta Tarayya, Dokta Ibrahim Jalo Daudu, ya  ga ’yan siyasar kasar nan cewa su yi koyi da magabatansu wajen ganin suna iya magance matsalolin da suke tasowa.

Dokta Jalo Daudu, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu inda ya ce magance matsaloli ne babban aikin da ’yan siyasa ya kamata su mayar da hankali a kai domin shi ne gaba da komai.

Ya ce duk wanda aka zabe shi a matsayin shugaba ya kamata ya yi koyi da halin Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello wajen yin duk mai yiwuwa don zama shugaba nagari irinsa ya zama abin koyi ga kowa musamman a yankin Arewa.

Dokta Jalo Daudu, ya kara da cewa a lokacin Sardauna komai yana tafiya daidai don haka bai ga dalilin da a yanzu abubuwa suke tafiya a karkace ba, inda rikice-rikice suka yi yawa shugabanni ba sa iya shawo kansu.

Ya ce “Sardauna shugaba ne mai adalci wanda al’ummar Arewa suke alfahari da shi saboda ya bar tarihi da a kowane lokaci za a ga jama’a suna kafa kungiyoyi da sunansa.

Me ya sa shugabanninmu na yanzu ba za su yi abin da za a rika tunawa da su kamarsa ba.”

Ya hori matasa kan su mayar da hankali wajen zabo shugabannin da za su shugabance su don gudun kada a zabo shugaban da bai da kishin al’umma sai kishin aljihunsa.

Daga nan Dokta Jalo Daudu, ya kalubalanci shugabanni a dukkan matakai su yi kokari su kamanta wajen gudanar da ayyukan da ko sun gushe za a tuna da su kamar yadda ake tunawa da Sardauna har  zuwa wannan lokaci.