✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici a Billa: Monguno ya sa zare da Abba Kyari

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro (NSA) Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tayar da kura a Fadar Shugaban Kasa, bayan da ya zargi…

Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro (NSA) Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya tayar da kura a Fadar Shugaban Kasa, bayan da ya zargi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Alhaji Abba Kyari da yi masa katsalanda a aiki, inda yake tsoma baki a harkokin tsaro ba tare da sanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba.

Janar Monguno ya yi wannan zargi ne a wata wasika da ya rubuta wadda kuma kafar labarai ta Premium Times ta bankado kuma ta fara wallafawa.

A wasikar, Janar Monguno ya ba manyan hafsoshin sojin kasar nan umarnin da su daina bin umarni da Abba Kyari ke ba su.

Fadar Shugaban Kasa ba ta ce komai ba kan batun har zuwa hada wannan rahoto, amma masana a harkar tsaro da suka tattauna da Aminiya sun bayyana cewa irin wannan sabanin zai kawo cikas ga harkokin tsaro wanda ke fuskantar matsala a baya-bayan nan.

Janar Monguno ya fadi a cikin wasikar cewa, wani lokacin da Abba Kyari yakan aika wa manyan hafososhin umarni wanda ba daga Shugaban Kasa ke zuwa ba, kuma ba tare da umarninsa ba, wanda a cewarsa yana cikin abin da ke dawo da hannun agogo baya a lamarin yaki da ta’addanci.

“Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa ba shugaban harkokin tsaro ba ne, kuma bai yi rantsuwa domin kare kasar nan ba. Don haka jagorantar tarurruka da manyan hafsoshin sojoji da shugabannin tsaro da jakadun kasashen waje ba tare da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro ko Ministan Tsaro ba, ya saba wa ka’ida, kuma hakan cin fuska ne ga Shugaban Kasa.

“Irin wadannan abubuwa da Shugaban Ma’aikatan yake yi, ba kawai ya bata lamarin ma’aikatun tsaro ba ne, har ma da mayar da hannun agogo baya a yaki da ta’addanci da tabbatar da tsaro da Shugaban Kasa ya sanya a gaba,” inji Monguno wanda Manjo Janar ne mai ritaya a cikin wasikar da ya rubuta a ranar 9 ga Disamban bara.

Wani tsohon Darakta a Fadar Shugaban Kasa wanda ba ya so a ambaci sunansa ya ce a tsari, Shugaban Ma’aikatan shi ne shugaba dukkan wadanda Shugaban Kasa ya ba mukami, kuma za a iya cewa mukaminsa ya fi na Mashawarcin Shugaban Kasa, amma sai ya ce ba ya da cikakkiyar masaniya a kan yana da damar gudanar da tarurruka da manyan hafsoshin soja ba tare da umarnin Shugaban Kasa ba.

Ya ce alhakin ofishin Shugaban Ma’aikatan ne ya tsara dukkan tarurruka da Shugaban Kasa, ciki kuwa har da tarurruka da manyan hafsoshin tsaro.

Ya ce sabani a tsakanin mutanen biyu an taba shawo kan lamarin a shekarun baya bayan an misalta tsarin da na Amurka, “A tsarin mulki na Amurka Shugaban Ma’aikatan yana sama da dukkan masu rike da mukamai. Shi mashawarcin ma ba a Fadar Shugaban Kasa yake ba.”

 

Sabanin tsakaninsu ba zai haifar wa Najeriya da mai ido ba

Wani tsohon sojan Najeriya wanda ya yi ritaya a matsayin Kanar ya ce sabani tsakanin mutanen biyu zai fi zama kalubale ga Najeriya sama da sauran kalubalen da ake iya gani.

“Ayyukan ofisoshin guda biyu sun bambanta, amma kuma sabani tsakaninsu matsala ce babba, musamman a lokacin da kasa ke fama da rikice-rikice. Irin wannan sabani ma zai iya jawo wa Shugaban Kasa abin kunya,” inji shi.

Tsohon sojan ya kara da cewa, Shugaban Ma’aikatan kamar sakataren mutum na kansa ne, kuma kawai nadi ne. Ba a bayyana shi a cikin kundin tsarin mulki ba kuma Shugaban Kasa ba ya bukatar amincewar Majalisar Dattawa wajen zaben wanda yake so ya rike masa wannan mukami.

“Mai rike da wannan mukamin ana so ne ya tabbatar da samun sauki wajen isar da sako a tsakanin Shugaabn Kasa da sauran masu rike da mukamai. Kuma yana cikin aikinsa kare martaba da mutuncin Shugaban Kasa, amma kuma ba ya rika yanke hukunci ko shawara kamar shi ne Shugaban Kasa ba, ko kuma ya rika fadin yadda sauran masu mukaman za su yi aiki yadda yake so.

“Shi kuma Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, yana ba Shugaban Kasa shawara ce kan harkokin tsaro. Dole ana bukatar amincewar Majalisar Dattawa wajen zabensa kamar ministoci. Shi ne ke jagorantar ayyukan duk wata ma’aikatar tsaro a kasa tare da tabbatar da cewa suna aiki tare. To idan har yana so ya yi aikinsa da kyau, dole ya kasance yana samun ganin Shugaban Kasa ba tare da wani tsaiko ba.

“Amma abin takaici, sabani a tsakanin Kyari da Monguno ya dade yana gudana. Sun yi sama da shekara uku ba sa ga maciji, kuma ina tabbatar maka cewa Mashawarcin Shugaban Kasan bai samun lamarin da sauki. Yanzu ne rikicin ya fito fili,” inji Kanar din.

Kanar din ya ce a ka’ida manyan hafsoshin tsaro ya kamata a ce suna ba Mashawarcin Shugaban Kasa bayani ne, “wanda shi ma tsohon Janar ne. Shi kuma zai kai bayaninsu ga Shugaban Kasa. Bai kamata manyan hafsoshin soja su rika ba Shugaba Ma’aikatan bayani ba wanda ma farar hula ne kuma ba ya da masaniya kan ayyukan soja,” inji shi.

Ya ce abin da Mashawarcin Shugaban Kasa ya fada a wasikar da aka bankado gaskiya ce, amma, “A Najeriya ba girman ofishin da kake rikewa ba ne, kusancinka da karfin ikon shi ne. Sannan kuma da Janar Monguno da Abba Kyari duk ’yan Jihar Borno ne, kuma bayan abin da ke faruwa a Abuja, suna wani abu a tsakaninsu a can gida Borno. Ya kamata Shugaban Kasa ya dauki mataki kan lamarin ta hanyar yin bayani a kan aiki kowane mai rike da mukami kafin abin ya yi kamari,’ inji shi.

Ya ce, “Yakin da ake yi da Boko Haram da barayin mutane da sauransu ba zai kare ba matukar Mashawarcin Shugaban Kasa da ba ya ga maciji da manyan na kusa da Shugaban Kasa, kuma lallai sai an yi wani abu game da lamarin, amma idan aka ci gaba da haka, ’yan Najeriya za su ci gaba da shan wahala kuma sojojinmu da ke filin daga ba za su samu nasarar da ake bukata ba.”

Aminiya ta tuntubi Fadar Shugaban Kasa domin karin haske kan lamarin, inda Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya ce babu wani haske dai zai kara a yanzu.

Shi ma Kakakin Hedkwatar Tsaro, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu cewa ya yi bai samu gamsasshen bayan kan lamarin ba, amma zai kara bincikawa.