✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici na neman yin gaba da Shugaban Jam’iyyar APC

Yayin da rikicin cikin-gida ke ci gaba da ruruwa a Jam’iyyar APC mai mulki, wadansu jiga-jigan jam’iyyar na ganin kamata ya yi Shugaban Jam’iyyar ta…

Yayin da rikicin cikin-gida ke ci gaba da ruruwa a Jam’iyyar APC mai mulki, wadansu jiga-jigan jam’iyyar na ganin kamata ya yi Shugaban Jam’iyyar ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya sauka daga mukaminsa, don samun maslaha da dorewar jam’iyyar.

Rikicin da ake ganin tamkar ’yan adawa ne ke yada jijta-jita a kai tare da kara rura shi, yanzu ya fara bayyana a fili, inda rashin jituwa a tsakanin Kwamared Adams Oshiomhole da wadansu gwamnonin jam’iyyar da ’yan jam’iyyar a jihohi yake kara kamari.

Da dama daga gwamnoni masu ci da kuma tsofaffin gwamnonin jam’iyyar da ’ya’yan jam’iyyar na ganin hanya daya da za a iya dinke wannan baraka ita ce shugaban ya sauka daga mukaminsa.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ta Kasa a Arewa, Sanata Lawal Shu’aibu, ya ce “Shugabannin jiha na jam’iyyarmu sun ce su ba su yarda ba sai Oshiomole ya tafi.”

Ya kara da cewa “Babu yadda za a yi jam’iyya ta ci gaba a haka saboda irin rabuwar kan da ke jam’iyyar ba abu ne da za a iya dinkewa cikin sauki ba.

“Tana dinkuwa amma sai dai da za a samu a ce (Oshiomhole) ya sauka, to da duk mai korafi zai daina,” inji shi.

To sai dai kuma wadansu jiga-jigan jam’iyyar na kasa sun ce batun kiraye-kirayen da ake yi Oshiomhole ya sauka daga kan mukami ba daidai ba ne.

Ibrahim Masari ya ce “Ko miskala zarratin Shugaban Jam’iyyar APC ba zai sauka ba, idan an kama shi da wani laifi ne to abin da za a yi shi ne kiran babban taron jam’iyya. Sai a zayyana duk laifuffukan da ake tuhumarsa da su a gaban wannan taro sannan a ce an sauke shi daga mukami idan an same shi da laifi.”

“Amma ba kawai rankadama wani mutum ya zo ya ce wai shugaban jam’iyya ya sauka ba,” inji shi.

Da yake sharhi kan lamarin a shashen Hausa na BBC, Landan Dokta Tukur Abdulkadir na Jami’ar Jihar Kaduna wanda masanin siyasar Najeriya ce ya ce dole ne shugabannin jam’iyyar su tsaya su kalli al’amarin su gyara.

Ya ce idan har ’ya’yan jam’iyyar ba su farka ba, to jam’iyya mai mulki na daf da rugujewa kuma bai zama lallai ta yi tasiri ba a zabe mai zuwa na shekarar 2023.

Sai dai Ibrahim Masari na Jam’iyyar APC ya yi inkarin hasashen rushewar jam’iyyar, inda ya ce rikicin da jam’iyyar ke ciki na nuna irin tumbatsar da ta yi ne.

“Ai kananan jam’iyyu ba sa samun rikicin gida, batun cewa Jam’iyyar APC na dab da rushewa abin ban dariya ne,” inji shi.

An zuba ido a gani ko Shugaba Muhammadu Buhari zai sa baki wajen ganin rikicin bai kai mizanin ruguza jam’iyyar ba.

A baya dai Shugaban ya sha cewa ba zai shiga lamarin da ba huruminsa ba, kafin daga bisani a ‘tilasta’ shi saka bakin mafi yawanci a lokacin da bakin alkalami ya riga ya bushe.