✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke tsakanin Messi da daraktan wasannin Barceloa Abidal

Lionel Messi ya caccaki Daraktan Wasanni na Kungiyar Barcelona, Mista Eric Abidal saboda ya ce wadansu ’yan wasa ba su sa kwazo a karkashin tsohon…

Lionel Messi ya caccaki Daraktan Wasanni na Kungiyar Barcelona, Mista Eric Abidal saboda ya ce wadansu ’yan wasa ba su sa kwazo a karkashin tsohon kocin kungiyar Ernesto Balberde ba.

A cikin watan Janairu Barcelona ta sallami Balberde ta maye gurbinsa da Kuikue Setien.

Abidal tsohon abokin kwallon Messi ne a kungiyar ta Barcelona, kuma ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar Diario Sports ta kasar Spain

Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, Messi ya mayar da martani, inda ya ce “Idan ka yi batu kan ’yan wasa ya kamata ka bayyana suna, saboda idan ba haka ba za ka samar da kafar da za a shafa wa kowa kashin kaji.’’

An kori Balberde a lokacin da Barcelona ke ta daya a kan teburin La Liga, Real Madrid wadda take ta biyu a lokacin, yanzu ta zama ta daya.

Messi ya kara da cewa ‘yan wasa ne ke da alhakin duk abin da ya faru a cikin fili, “Kuma mu ne na farko da muka fi sani idan ba mu taka rawar gani ba. Ya kamata bangaren mahukuntan kungiyar shi ma ya dauki alhakin dukkan abubuwan da suke faruwa da hukuncin da ya dauka,” inji shi.

A wata hirar da aka yi da Abidal a Diario Sports ya ce ‘“Ina jin Messi yana jin dadin zama a Barca an kuma tanadi sabuwar yarjejeniya da ake tattaunawa da dan wasan,” kamar yadda BBC ya ruwaito.