✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC: Na koyi darasi –  Adams Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya koma kan kujerarsa a ranar Talatar da ta gabata bayan mako biyu da dakatar da shi…

Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya koma kan kujerarsa a ranar Talatar da ta gabata bayan mako biyu da dakatar da shi daga shugabancin, inda ya ce ya koyi darasi.

Wata Babbar Kotun Abuja ce, ta dakatar da shi daga shugabancin jam’iyyar a ranar 4 ga Maris, inda a ranar Litinin da ta gabata kuma Kotun Daukaka Kara ta soke dakatarwar.

Kwamared Oshiomhole ya shugabancin zaman Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar ta Kasa (NWC), a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Talatar. Bayan zaman kwamitin na awa biyar Oshiomhole ya bayar da sanarwar janye dakatarwar da aka yi wa Na’ibin Shugaban Jam’iyyar ta Kasa (shiyyar Arewa) Sanata Lawal Shu’aibu da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (a Arewa maso Yamma), Alhaji Inuwa Abdulkadir.

Dakatar da Sanata Shu’aibu da Abdulkadir da Kwamitin NWC karkashin Oshiomhole ya yi na daga cikin abubuwan da suka jawo rikici a cikin jam’iyyar.

Wakilan Kwamitin NWC da ake zargin suna adawa da Oshiomhole sun hada da Mukaddashin Sakataren Jam’iyyar ta Kasa Cif Bictor Giadom da Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu maso Yamma, Bankole Oluwajana da takwaransa na Arewa maso Gabas Mustapha Salihu da Mataimakin Sakaytaren Watsa Labarai Mohammed Ibrahim da kuma Alhaji inuwa Abdulkadir.

Oshiomhole ya ce an yanke shawara kan wakilan Kwamitin NWC biyu ne a wani mataki na slhuntawa da jam’iyyar ke yi. Ya ce jami’an biyu yanzu sun koma bakin aiki. “Na rokon kowa kan ko mene ne suke ganin gazawata su yi min gafara, kuma sun gafarta min. Ni ma duk abin da nake ganin gazawar wani ne na gafarta masa, kuma ina da yakinin wannan ce hanyar samar da shugabanci nagari kai a hade.

Tun farko lokacin da yake jawabin bude taron Oshiomhole ya ce attaunawa ce makamin yaki da zarge-zarge, inda ya yi alkawarin ba zai nuna son kai a shugabancinsa yana  mai cewa yana sane da cewa itaciya daya ba ta isa samar da gandun daji.

Ya ce ba shi ne shugaban da ya fi kowa ba, kuma ba zai zama haka ba, amma yana jin babu wanda zai soke shi game da kyakkyawar niyyarsa ta samar da shugabanci nagari.