✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci ya yi sanadiyar mutuwar mutum 4 a Lamurde

Rikicin kabilanci a tsakanin kabilun Waja da Lunguda mazauna garin Lafiyar Lamurde da yankin Bachikiri a Jihar Adamawa ya ci rayuka hudu sannan wadansu daruruwan…

Rikicin kabilanci a tsakanin kabilun Waja da Lunguda mazauna garin Lafiyar Lamurde da yankin Bachikiri a Jihar Adamawa ya ci rayuka hudu sannan wadansu daruruwan magidanta sun yi gudun hijira.

Rikicin da ya faru ya yi sanadiyar jawo munanan raunuka ga wadansu matasa, sannan ya raba wadansu da dama da matsugunnansu, inda suka yi hijira zuwa garin Bambam na Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Magidantan da ’ya’yansu sun yi gudun tsira ne inda suka yi tattaki na tsawon kilomita 50 a kasa, daga Lafiyar Lamurde zuwa Bambam.

Mutanen suna zaune ne a makarantar Firamare ta Central ta garin Bamban a matsayin sansani kafin lafawar rikicin.

Wata majiya ta Red Cross da ta sanar da wakilinmu labarin faruwar rikicin, ta ce ba za ta yi wani karin haske ba har sai ta samu izini daga Abuja.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) kan faruwar rikicin, amma lamarin ya ci tura. Har zuwa lokacin aiko da wannan rahoto wakilinmu bai samu cikakke bayani kan musabbabin faruwar rikicin ba.