✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kirkiro masarautu a Jihar Kano ya dauki sabon salo

A Jihar Kano lokacin da ake ta cacar baki a tsakanin masu nuna goyon baya da wadanda ke nuna adawa da  sake kirkiro sababbin masarautu hudu,…

A Jihar Kano lokacin da ake ta cacar baki a tsakanin masu nuna goyon baya da wadanda ke nuna adawa da  sake kirkiro sababbin masarautu hudu, wato masarautun Bichi da Rano da Gaya da Karaye da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya yi daga Masarautar Kano a kwanan nan, bayan da ya sake samun sahalewar Majalisar Dokokin Jihar na amincewa da dokar kirkiro da sababbin masarautun, bayan ta yi gyara a kundin dokar nadawa da tube Sarki a jihar.

Sanadiyyar haka, yanzu kuma dukkan sababbin majalisun masarautun sarakunan a wani zama da suka gudanar a hedkwatocin masarautunsu wato Bichi da Rano da Gaya da Karaye a ranar Juma’ar da ta gabata, sun ba da shelar tube rawunnan wasu hakimai 18, da ke cikin masarautunsu da suka hada da masu zaben Sarkin Kano hudu wato Madakin Kano kuma Hakimin Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Nabahani da Makaman Kano kuma Hakimin Wudil Alhaji Abdullahi Sarki Ibrahim da Sarkin Bai Alhaji Mukhtari Adnan (wanda ya shafe shekara 64, a kan karagar mulkin gundumar Dambatta) da Sarkin Dawaki Mai Tuta kuma Hakimin Gabasawa Alhaji Bello Abubakar.

Su wadannan hakimai hudu, tun cikin watan Mayun da ya gabata suka  garzaya gaban Mai shari’a Usman Na’abba na Babbar Kotun Jihar, suna kalubalantar kafa dokar kirkiro sababbin masarautun hudu da kuma nada sarakunan. Masarautar Rano ita ta fi sallamar kakimanta mafi yawa, inda ta sallami 6 daga cikin 10 da take da su. Wadanda aka sallama sun hada da Hakimin Tudun Wada da na Doguwa da na Kura da na Garun Malam da na Takai da na Bebeji.

Hakiman Kibiya da na Sumaila da na Bunkure da ita kanta Ranon su kadai masarautar ta Rano ta tabbatar da mubayi’arsu ga masarautar da ita kanta gwamnatin jihar.

Daga masarautar Bichi kuwa, hakimai biyar suka rasa rawunansuu da suka hada da Hakimin Dambatta da na Dawakin Tofa (dukkansu masu zaben Sarkin Kano), sai Hakimin Tsanyawa da na Bichin kanta da na Minjibir.

Daga Masarautar Gaya ma hakimai biyar masarautar ta sallama, wadanda suka hada da Hakimin Wudil da na Gabasawa (su ma masu zaben Sarkin Kano), sauran  su ne Hakimin Warawa da na Gabasawa da na Dawakin Kudu da na Garko.  Masarautar Karaye ce kadai ta sallami hakimai biyu, na Rimin Gado da na Kiru.

Dukkan majalisun masarautun hudu nan take suka bayyana sunayen wadanda suka maye gurbin hakiman da aka tube. Dadin-dadawa duk laifuffuka iri daya masarautun suka zargi tubabbun hakiman nasu da aikatawa. Laifuffukan da suka hada da kin yin mubayi’a ga sababbin sarakunan tare da bijire wa duk wani umarni, walau daga sarakunan ko daga ita kanta gwamnatin jihar.   Kamar yadda aka sani al’ada ce ga sarakuna a kasar Hausa, duk wanda yake dauke da rawani a wata masarauta, musamman hakimai da dagatai zuwa masu unguwanni, muddin aka nada sabon Sarki ba su kai caffar mubayi’a ba, bare kuma  ya rika yin fito-na-fito da sabon Sarkin ko gwamnatin jiha, Sarki ka iya warware masa rawaninsa, ya nada mai biyayayya gare shi da gwamnati.

Tun bayan da Majalisar Dokokin Jihar ta yi waccan doka ta farko da Gwamna Ganduje ya nada sababbin sarakunan a watan Mayun da ya gabata da rusa sarakunan da Mai shari’a Na’abba ya yi cikin watan Satumban da ya gabata, mutane musamman ’yan jihar suka shiga cece-ku-ce a kan dacewa da rashin dacewar kirkiro sababbin  masarautun.

Wadanda suke kan gaba wajen nuna adawa da kirkiro masarautun sun hada da masu zaben Sarki na Masarautar Kano da na ambaci sunayensu a sama, wadanda don nuna cikakkiyar kin amincewa da sababbin sarakunan har kotu suka garzaya, inda suka shigar da karar ba su amince ba. Karar da har zuwa wannan karo na biyu da Majalisar Dokokin Jihar ta sake amincewa da wata sabuwar dokar kirkiro da sake nada sababbin sarakunan hudu kuma Gwamna Ganduje ya sake nada wadancan sarakuna hudun kotun ba ta yanke hukunci a kanta ba.

Akwai kuma Kungiyar Masu Muradin Kare Kano wato Kano Concern Citizens Initiatibe da take karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa da kuma wasu malaman jami’a da na addinin Musulunci da dukkansu ba su amince da kirkiro sababbin masarautu a Jihar Kano ba. Hujjojin da akasari suke kafawa sun hada da yadda yin hakan zai kawo rarrabuwar kawuna da rashin jituwa a tsakanin mutanen jihar da suke da addini da al’ada da dabi’a da harshe duk iri daya. Dadin dadawa kuma masu kin jinin kirkiro masarautun suna kafa hujja da cewa ko da Bature ya ci Kano da yaki, daya daga cikin yarjejeniyar da aka yi da shi, shi ne ba za a taba raba Kano ba. Amma kuma wadansu na da tambaya a kan masu irin wancan ra’ayi a kan suna ina a 1991, aka yi wa Masarautar Kanon ayaga ta hanyar hada wasu hakimai da ke cikin Masarautar Kano  da a yau suka zama Masarautun Dutse da Ringim a cikin sabuwar Jihar Jigawa?

Da farko waccan kungiya ta Kano Concern Citizens Initiatibe, a kungiyance ita  kadai take adawa da kirkiro wadancan masarautu, amma a yanzu an sake samun wata kungiya da ta kira kanta da Kungiyar Kanawa masu Mutunci, wato Kano Integrity Forum karkashin jagorancin Farfesa Abdu Salihi, tsohon Kwamishina a gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau. Kungiyar da ta bayyana wa duniya cewa tana goyon bayan kara kirkiro masarautun da aka yi a jihar.

A wani taron manema labarai da shugabannin kungiyar suka kira a Kano a makon jiya an ji shugaban kungiyar Farfesa Salihi yana cewa suna goyon bayan kirkiro sababbin masarautun dari bisa dari, har ya ba da hujjojinsu na yin haka.

Na daya, ya ce kirkiro masarautun zai samar da ayyukan yi ga dimbin matasan jihar baki daya. Na biyu, sababbin masarautun za su ba da dama wajen kara bude yankunan karkara su samu bunkasar abubuwan more jin dadin rayuwa irin su asibitoci da manya da kananan makarantu da sauransu. Hatta matakan tsaro za su samu bunkasa, inji Farfesa Salihi.

Da yake mayar da martani a kan masu sukar kirkiro sababbin masarautun har suna kafa hujja da tarihi, Farfesa Abdu Salihi cewa ya yi irin wadancan mutane, mutane ne da suka yi imani da tarihi, amma kuma ba sa tare da abin da ke cikin tarihi. Yana mai cewa “Irin wadancan mutane sun rufe idanunsu a kan tarihi kawai, amma sun manta da cewa za a iya zama da tarihi ne kawai zuwa wani lokaci.”

Ka iya cewa ko kusa babu dadi a ce wannan al’amari da ya kamata kowa ya kalle shi da idon basira, kamar yadda ’yan Majalisar Dokokin Jihar  37, in ban da mutum 1, suka amince da dokar kara kirkiro masarautun (duk da a yanzu Jam’iyyar APC na da mambobi 25 ta PDP na da 12), amma a tashi daya al’amarin ya ci hakimai masu kasa har 18, abin da ba a taba yi ba a tarihin Masarautar Kano. Kamar yadda na fadi a wannan shafi bayan kirkiro da masarautun a karon farko cikin watan Mayun da ya gabata, mutanen karkara dai suna son sababbin masarautun su zauna daram-dam, yayin da wasdanu mutanen cikin birnin Kano suke yin adawa.

Ina ma a ce Gwamna Ganduje zai gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a a zaman kuri’ar raba gardama a jihar?