Daily Trust Aminiya - Rikicin Kwalejin Malikiyya: Dalilin da ba mu biya kudaden ma
Subscribe

Rikicin Kwalejin Malikiyya: Dalilin da ba mu biya kudaden makarantar dalibai 1000 ba – Kwamishina Zaki

Alhaji Abdulrazak Nuhu Zaki shi ne Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Bauchi, a zantawarsa da ’yan jarida ya bayyana dalilin da ya sa gwamnati ba ta biya wa daliban Kwalejin Malikiyya kudaden da ya kamata ta biya musu:

Daliban Kwalejin Malikiyya na korafin cewa gwamnati ta gaza biyansu kudaden makarantarsu?

Ita wannan makaranta ta Kwalejin Malikiyya, makaranta ce da ba a santa ba a kasar nan, ba a tantance ta ba, yaya za mu biya kudaden al’umma ga makarantar da babu wanda ya santa. Daliban makarantar ma ba sa iya yin jarrabawa a makarantar alhali mun yi alkawarin cewa za mu kashe kudaden al’ummar Jihar Bauchi cikin gaskiya da adalci.

Masu makarantar na ikirarin cewa alkawari suka yi da gwamnatin baya don a rage yawan karancin malaman jinya a jiha?

Ni kaina tsohon ma’aikacin jinya ne, na sa ’ya’yana biyu a wannan makaranta amma sai da na yi da-na-sani don ba wajen da za su iya yin jarrabawa su kammala sai da na nema musu wata makaranta sannan suka dauki jarrabawar. Don haka muka ce ba za mu biya ba don makarantar ba sananniya ba ce. Ai muna da makarantu da yawa a Jihar Bauchi na gwamnati da ya kamata dalibai su yi kamar Makarantun Koyon Aikin Jinya da Ungozoma na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma na Gwamnatin Jihar Bauchi. Akwai Kwalejin Kiwon Lafiya da ke Ningi akwai kwalejojin kimiyya na tarayya da na jiha.

Amma daliban makarantar ’yan asalin Jihar Bauchi ne?

Ka san dai makarantar mai zaman kanta ce, gwamnati kuma tana biyan makarantun gwamnati ne, idan su daliban ’yan Jihar Bauchi ne sai su nemi alawus daga gwamnatin jiha wato scholarship amma ba kudin Ma’aikatar Kananan Hukumomi ba. Ka san Gwamnan Jiharmu na yanzu yana da kishin ilimi kwarai da gaske.

Ana zargin gwamnati cewa tana rike kudaden kananan hukumomi?

Amma ba wannan gwamnatin ba, kudaden kananan hukumomi asususn kananan hokumomin suke tafiya kai-tsaye sai dai in akwai ayyuka na musamman da za su rika gudanarwa, wajibi ne mu sa ido mu ga cewa ayyukan sun bi dukkan ka’idodin da suka kamata. Ba don wannan hadakar ayyukan da ake yi tsakanin Gwamnatin Jihar da kananan hukumomin ba ko albashi wasu kananan hukumomin ba za su iya biya ba, saboda mawuyacin hali na bashi da aka sa su a ciki duk da irin dimbin kudaden da Gwamnatin Tarayya ta ba su.

Yanzu mece ce makomar wadannan dalibai?

Makomarsu ita ce suna makaranta ce mai zaman kanta, kuma duk wanda yake makaranta mai zaman kanta ya san zai iya ne ya shiga irin wannan makaranta. Amma haka kawai ba za mu dauki kudaden jiha mu bai wa mutum guda shi kadai ba, ba tare da mun tabbatar da cewa makarantar kowa ya santa ba kuma ta cika dukkan ka’idodi ba.

texem
More Stories