Search
Subscribe
Rikicin makiyaya da manoma ya ci rayukan Fulani 12 a Kogi

Rikicin makiyaya da manoma ya ci rayukan Fulani 12 a Kogi

Al’ummar Fulani a kananan hukumomin Yagba ta Yamma da Dekina da Igalamela da Omala da ke Jihar Kogi sun koka kan wani rikici da suka ce ya ci rayukan Fulani makiyaya 12 yayin da wadansu da dama suka bace. Sakataren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a yankin, Malam Muhammadu Mainasara ya shaida wa Aminiya cewa, a ranar Asabar din makon jiya wani basarake a yankin ya kira shi ta waya inda ya shaida masa cewa, an kashe wani manomi kuma ana zargin Fulani makiyaya ne suka kashe shi. “Ko da na ji haka sai na fara bincikar mutanenmu domin tabbatar da gaskiyar lamarin amma kafin mu farga sai labari ya iso mana cewa, mutanen na can sun tare hanya a wani gefen fada, duk inda suka ga Bafulatani sai su hau shi da sara su kashe zuwa yanzu mun gano gawarwakin Fulani 12 mun yi musu sutura, sai da muka kwashe kwana uku muna aikin nemo gawarwaki a daji domin in sun kashe su sai su daura musu dutse su jefa a ruwa,” inji shi.

Ya ce, Gwamnan Jihar Alhaji Yahaya Bello, ya kira su taron gaggawa na zaman lafiya inda ya ba su tabbacin cewa za a zakulo wadanda suka aikata ta’asar.

Shugaban Matasan Fulanin yankin Alhaji Babuga Mairali kira ya yi ga Fulanin yankin su yi hakuri su guji daukar doka a hannu ko  daukar fansa, su kyale hukuma ta yi aikinta, “Mun yi gargadi ga mutanenmu cewa, su yi hakuri su guji daukar fansa, domin ba ma son abin da ke faruwa a wasu wurare ya faru a nan. Mu mutane ne masu son zaman lafiya, wannan  jarrabawa da ta same mu, ta dame mu kwarai, kirana ga mahukunta su dauki mataki, kamata ya yi wakilan gwamnati a matakin tarayya da  jiha su zo su ga yadda lamarin ya faru su agaza mana.” inji shi.

A nasa bangaren Sarkin Fulanin yankin, Malam Muhammadu Kiruwa Burutu ya shaida wa Aminiya cewa, a baya ba su taba ganin irin wannan rikici ba. Ya ce, ya shafe sama da shekara 56 a yankin amma ba a taba samun mummunan rikici kamar wannan ba, don haka ya yi kira ga mahukunta su dauki matakin kashe wutar rikicin

Gwaman Jihar Kogi ya yi taron gaggawa na zaman lafiya tare da Fulani da manoma da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar tsaro a jihar a fadar gwamnatinsa da ke Lakwaja inda ya sha alwashin tube shugabannin gargajiya da na kananan hukumomi 4 da lamarin ya auku a cikinsu muddin ba su binciko wadanda suke da hannu a aika-aikar ba.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kogi, Hakim Busari, ya ce ya tura jami’an runduna ta musanmman domin tabbatar da tsaro a yankunan da rikincin ya auku. Zuwa yanzu dai rundunar ta kama mutum 16 da ake zargi da hannu a lamarin ciki har da ’ya’yan kungiyar sa-kai ta bijilante su tara.

 

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin