✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma da makiyaya: An kaddamar kwamitin sake tsara labin shanu

A ranar Talatar makon da ake ciki ne shugaban karamar hukumar Jama’a, Alhaji Yusuf Usman Mu’azu ya kaddamar da kwamitin lura da labi-labi na dabbobi…

A ranar Talatar makon da ake ciki ne shugaban karamar hukumar Jama’a, Alhaji Yusuf Usman Mu’azu ya kaddamar da kwamitin lura da labi-labi na dabbobi don sake bude su kafin saukar damina mai zuwa don magance rikice-rikicen da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya.

Shugaban ya bayyana a lokacin kaddamarwar da ta gudana a sakatariyar karamar hukumar cewa lura da irin matsalolin da ke tasowa tsakanin makiyaya da manoma ba wanda ba komai ba ne ke haifar da shi face yin watsi da hakkokin juna.

“Kowa ya san a shekarun baya babu irin wadannan matsalolin amma yanzu manoma sun toshe labin da tuntuni a ka san hanyar wucewar dabbobi ne. To aikin wannan kwamiti ne sake duba duk wuraren da aka san hanyar dabbobi ne don sake bude shi kafin saukar ruwan sama na bana tunda an gama girbi a halin yanzu. Mun rubutawa gwamnatin jiha wannan buri namu shine a halin yanzu da suka bamu dama mu ke kaddamar da wannan kwamiti wanda muna sa ran za su yi aikinsu tsakani da Allah don samar da zaman lafiya da fahimtar juna.”

A lokacin da yake mayar da martini, shugaban kwamitin, Dakta Billy Ishaya la’ah ya nuna jin dadinsa da samun irin wannan ci gaba tare da alkawarin yin aiki tukuru kuma tsakani da Allah.”

Kwamitin mutum goma sha takwas, sun kunshi wakilai daga kungiyar manoma da na Miyetti Alllah da shugabannin sashin noma da na gandun daji da wakilan sarakunan gargajiya da na jami’an tsaron SSS da DSS da ‘yan sanda da hukumar shige da fice da sauransu.   

A wata sabuwa kuma shugaban karamar hukumar ta Jama’a a madadinsa da ‘yan majalisarsa sun baiwa shugaban ‘yan sandan yanki na Kafanchan (DPO) lambar girmamawa saboda irin kwazon da yake nunawa wajen samar da zaman lafiya a yankin na kafanchan.

Karramawar, wacce ta gudana a sakatariyar karamar hukumar jim kadan bayan kaddamar da kwamitin, ta samu halartar DPOn tare da sauran masu rufa masa baya.

A lokacin da yake jawabi yayin mika lambar yabon, Alhaji Yusuf Usman Mu’azu, ya bayyana DPOn a matsayin mutum mai kokari wanda a kadayaushe yake bayar da duk gudummawar idan an sanar da shi wani abu ba tare da gajiyawa ba.

Lokacin da yake mayar da martini, DPO Baba Ali ya nuna farin cikinsa da lura da irin gudummawar da yak e bayarwa da ta sa aka karrama shi sai dai ya ce aikin samar da tsaro ba aiki ne na mutum daya ba, don haka ya yabawa shugaban karamar hukumar da irin goyon baya da yake basu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.