✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma da makiyaya: Masani ya ba da shawarar bullo da tsarin kiwon killace dabbobi

Wani masani Farfesa Oluwafemi Onifade, ya ba da shawarar a bullo da tsarin killace dabbobi a waje guda don yin kiwo da nufin magance rikicin…

Wani masani Farfesa Oluwafemi Onifade, ya ba da shawarar a bullo da tsarin killace dabbobi a waje guda don yin kiwo da nufin magance rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakanin manoma da makiyaya a kasar nan.

Farfesa Onifade wanda yake koyarwar a sashen kula da harkokin wuraren kiwo a Jami’ar Ayyukan Gona da ke Abeokuta, ya bayyana haka ne a wani taron kara wa juna sani tare da musayar bayanai da aka gudanar a Lakwaja fadar Jihar Kogi.

Ya bayyana cewa, tsarin killace dabbobin  waje guda zai bayar da damar a shuka amfanin gona tare da gudanar da noman a waje guda, inda ya ce  hakan zai kawo karshen riginginmu da rasa rayukan da ake yi mai nasaba da kiwon dabbobi.

Masanin, wanda kuma kwararren jami’in tuntuba ne a Kamfanin Synergos, ya ce binciken da aka gudanar a lokuta da dama, ya bayyana tsarin killacewar da zaman mai matukar tasiri ta fuskar wanzar da zaman lafiya a tsakanin manoma da makiyaya.

A cewarsa, an jarraba tsarin a wasu wurare uku da aka zaba a jihohin Kogi da Kaduna da Benuwai don zama zakaran gwajin dafin tsarin, kuma abin ya samu gagarumar nasara.

Farfesan ya ce wannan dabarar ta hadar da horar da manoma da makiyaya kan muhimmancin bangarorin sana’o’in nasu, da za su jawo musu gwaggwabar riba da alfanu.

Wani jami’in bincike da nazari na Kamfanin Synergos, Dokta Monele Saleh, ya ce baya ga kawar da rikice-rikice, tsarin zai kara bunkasa tattalin arzikin manoman da makiyayan. Sai ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai su jarraba tsarin.