✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin matasa: An tsaurara tsaro a Jos jihar Filato

Rahotanni na bayyana cewa, an samu wani rikici da ya barke a yankin Dutse Uku, gadar Cele Bridge da unguwar Rikkos a karamar hukumar Jos…

Rahotanni na bayyana cewa, an samu wani rikici da ya barke a yankin Dutse Uku, gadar Cele Bridge da unguwar Rikkos a karamar hukumar Jos ta Arewa da ke jihar Filato.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, wasu matasan yankin sun yi ta kone gidajen jama’a, ya zuwa yanzu ba a tabbatar da dalilin wannan rikicin ba. Sai dai an samu rahoton ganin gawar wani matashi a Anguwan Damisa da ke Dutse Uku.

Wani mazaunin unguwar ya shaidawa majiyarmu cewa, a yau an girke jami’an tsaro yankin.