✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Nyako da Bamanga ya dauki sabon salo

Bayan dakatar da gwamnonin Ribas da Sakkwato da uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta yi makonni biyu da suka gabata a yanzu kallo ya koma…

Bayan dakatar da gwamnonin Ribas da Sakkwato da uwar Jam’iyyar PDP ta kasa ta yi makonni biyu da suka gabata a yanzu kallo ya koma kan Gwamnan Jihar Adamawa Murtala H.Nyako da dama suka dade suna takun-saka da shugaban Jam’iyyar na kasa Alhaji Bamanga Tukur.
Wannan yana cikin wani shirin karkashin kasa da magoya bayan Gwamna Nyako sukace  sun bankado kan yunkurin korar Gwamnan da wasu manyan magoya bayansa daga jam’iyyar baki daya.
Mista P.P. Elisha shi ne Sakataren Jam’iyyar PDP a jihar bangaren Gwamna Nyako ya shaida wa manema labarai cewa Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Bamanga Tukur ya shirya wani kulli a karkashin kasa da nufin korar Gwamna Nyako da wasu gwamnonin da ake jin ba su zabi Gwamna Jonah Jang a matsayin shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya ba.
Ya ce abin takaice ne ganin yadda PDP take dakatar da gwamnoninta alhali a daya bangaren jam’iyyun adawa suna kokarin kafa kakkarfar jam’iyya da za ta kalubalanci PDP a zaben 2015. Ya ce wannan lokaci ne da ya kamata Jami’iyyar PDP ta maida hankali kan kalubalen da ke gabanta amma ba kori manyan shugabanninta ba.
Sakataren ya ce dakatar da Gwamna Rotimi Amaechi da Gwamna Magatakarda Wammako da jam’iyyar ta yi abin bakin ciki ne a irin wannan lokacin da kalubale ya kewaye jam’iyyar ba a bi ka’ida ba, domin ya saba wa sashi na 57 karamin sashi na 6 da ya tabbatar da cewa jam’iyyar ba za ta dauki irin wannan mataki ba tare da ta kafa kwamitin bincike a kan wanda ake zargi ba.
Ya ce amma abin takaici wadannan gwamnoni biyu uwar jam’iyyar ba ta bi wadannan matakai ba duk da irin matsayin da suke da shi a idon jama’ar jihohinsu.