✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin siyasar Jihar Ribas babbar barazana ce ga mulkin dimokuradiyya

Shugaban jam’iyyar PSP na Jihar Filato kuma Matawellen Toro, Alhaji Baban Iya Muhammad Umar ya bayyana cewa rikicin siyasar da ke faruwa a Jihar Ribers…

Alhaji Baban Iya Muhammad UmarShugaban jam’iyyar PSP na Jihar Filato kuma Matawellen Toro, Alhaji Baban Iya Muhammad Umar ya bayyana cewa rikicin siyasar da ke faruwa a Jihar Ribers wata babban barazana ce ga dorewar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya.
Alhaji Baban Iya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos.
Ya ce duk masu kaunar Nijeriya suna bakin ciki da rikicin siyasar da ke faruwa a jihar ta Ribers, wata babbar damuwa ce ga Najeriya.
Ya yi kira  ga gwamnatin tarayya ta dauki matakai na magance wannan rikicin siyasa, don kauce wa abubuwan da za su biyo bayansa.
Har ila yau ya nuna damuwarsa kan rikicin da ke faruwa tsakanin shugaban kasa da gwamnoni, lamarin da ya ce ya kamata su hada kai, domin su kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba a Najeriya, amma abin bakin ciki hakan yana neman ya gagara.
Alhaji Baban Iya Muhammad ya yi bayanin cewa  ya kamata shugaban kasa ya san cewa dukkan  gwamnonin Najeriya kamar ’ya’yansa ne, don haka ya yi kokari ya hada kan gwamnonin domin kasar ta sami zaman lafiya.
Daga nan ya yi kira ga ’yan siyasa da sauran shugabannin Najeriya su tsaya su natsu su hada kan kasa, don ganin an gudanar da  zabubbukan shekara ta 2015 lafiya, ba tare da samun wani tashin hankali ba.