✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Tafkin Chadi ya daidaita mutum fiye da miliyan biyu-Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo a jiya ya shaidawa tawagar Cibiyar Tabbatar da Zaman Lafiya da Tsaro ta Afirka cewa rikicin da ake yi a…

Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo a jiya ya shaidawa tawagar Cibiyar Tabbatar da Zaman Lafiya da Tsaro ta Afirka cewa rikicin da ake yi a yankin tafkin Chadi ya haifar da ’yan gudun hijira kimanin miliyan biyu da digo hudu.
Ya bayyana cewa rikicin ya haifar da asarar dukiya da gidaje da gonaki da kuma gine-ginen makarantu.
“A wasu lokutan lamarin na bukatar a sake gina illahirin gari”. Inji shi.
Osinbajo ya yi furucin ne yayin da ya karbi tawagar cibiyar karkashin jagorancin Ambasada Bankole Adeoye wanda har ila yau shi ne Jakadan Nijeriya a kasar Habasha da kuma Kungiyar Hadin Kan Afirka ta (AU).