Search
Subscribe
Rikita-rikitar Najeriya: Rana zafi inuwa kuna!

Rikita-rikitar Najeriya: Rana zafi inuwa kuna!

Ganin irin sabatta-juyata da ake ta yi da talakan Najeriya, irin yadda matsaloli suka yi masa yawa, ya sa GIZAGO (08065576011) ya haska fitilarsa a wannan bangare na talaka a kasar nan. Shin wane hali talakan Najeriya yake ciki? Ku biyo tsokacin Gizago:

 

Talaka bawan Allah! Shin wai ina ma wannan bawan Allah zai sanya kansa? Najeriya dai ta zama tamkar wani mugun fage, wanda ke baibaye da abubuwan firgici da tsoratarwa! “Rana zafi, inuwa kuna.” Abin da na ji wani talaka na fadi ke nan a kwanakin baya, lokacin da al’amuran rayuwa suka yi masa daurin gwarmai.

A yau dai talaka a Najeriya bai ma san babin da yake ciki ba. Kada ka yi maganar yunwa a kusa da shi, domin kuwa abin da ke gabansa ma ya fi karfinta. A lokacin da hamshakin attajirin da ke makwabtaka da shi ya saye tilon gonarsa, ya gina gidan mai. Tun daga lokacin ya daina turza dan noman da ke samar masa damman hatsin da ba su iya kai shi koda wata biyu.

A kullum ya fita neman aikin karfi, ba kasafai yake samu ba, saboda tulin matasan da suka mayar da kansu leburori, don haka sun tsare masa damar da zai samu wani aiki. Yakan dubi tulin matasa nan cikin takaici, ya ce: “Ai kuwa kamata ya yi a ce matasan nan suna makaranta domin neman ilimi.”

Ya mance da cewa babu yadda za a yi irin wadannan matasa su kasance a makaranta, domin kuwa ba su da kudin da za su biya diyyar da ake gindayawa a makarantun. Bai san ma da cewa wadansu matasan ma har jami’a sun gama ba, amma rashin abin yi ne ya tilasta musu dole su fita aikin leburanci, domin neman abin sawa a bakin salati.

Ran nan ya fita waje, sai ya ji wani a dandali yana ta bayyana abubuwan takaicin da ke addabar al’ummar kasar nan, musamman ma dai talakawa. Mutumin ya zo batun asibiti, sai ya ji yana cewa: “A yau dai asibitocinmu sun koma wajen yin allurar Foliyo. Wannan allura ce kawai ake yi wa yara kyauta, a yayin da koda Panadol majinyaci ke bukata, sai ya saya. Idan bai da kudin kuwa sai dai ciwon ya yi yadda yake so da shi.”

Kaico! Su kuwa wadanda muke kira shugabanninmu, wadanda muka sha zafin rana da tsananin sanyi da dukan ruwan sama, muka zabe su domin su kyautata mana, sai suka juya mana baya, suka kasance kuraye. Abin da suka iya kawai shi ne su kasafta dukiyar kasa a tsakaninsu. Ciwon kai idan ya kama su, sai su arce zuwa kasashen Turawa domin neman magani.

Bayan talauci, rashin aiki, cututtuka da sauran matsaloli da suka yi wa talakan Najeriya cacukwi, sai kuma a bangare daya aka hana shi zaman lafiya da kajagan ransa da ke lilo a jikinsa. Ga shi dai zaluncin shugabanni ya haddasa tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na kasar nan. Da ka ji bam ya tashi, rayukan talakawa za ka ji sun salwanta babu adadi! A yanzu ba bam kadai ake dana masa ba, wadansu ne ke hawa babura su same shi har gidansa, su kama shi su tafi da shi har sai an kai kudin fansa. Haka kuma, maharan su yi wa ’ya’yansa da matansa fyade, su kona masa gidan gaba daya.

A lokacin da talaka zai shiga matsala, abin kaddara ya sanya ya saci akuyar Naira dubu uku, sai alkali ya daure shi gidan kaso na shekara uku. A yayin da kuma wani jami’in gwamnati ya yi rub-da-ciki da biliyoyin kudin al’umma, nan take za a ba shi beli, ya tafi kuma yana wandaka da dukiyar nan. Babu abin da zai same shi, sai ma idan ta dauro ka ji sarkin garinsu ya nada shi wata babbar sarauta a fadarsa. Kaico!

A lokacin da karamin ma’aikaci ya yi ritaya daga aiki, daga nan ne matsalarsa ta fara sabuwa. Ba za a biya shi hakkokinsa ba, sai dai a bar shi da rigima tsakaninsa da masu gidan haya. A lokacin nan kuma za a kori ’ya’yansa daga makaranta, saboda rashin biyan kudin makaranta. Idan bai yi sa’a ba, har ya kai ga shiga kabari, babu wanda zai ba shi ko kwabo a matsayin kudin sallama.

Duniya mai abin mamaki! A lokacin da aka haramta wa wannan karamin ma’aikaci hakkokinsa, a lokacin ne kuma wani zai dunkule Naira bilyan biyu daga asusun al’umma, ya jera su a cikin dakin katafaren gidan da ya gina da dukiyar al’umma!

Shi ke nan, talaka ya zama tamkar abin farauta. Ko’ina ya shiga babu sai’ida sai tsoro da tsibin matsaloli da abin tsoro! To wane ne zai kawo masa dauki? Ni dai a ganina, babu wani mutum na farko da zai fara tallafa masa sai shi kansa da kansa.

Lallai ne talaka ya san ciwon kansa, ya dawo daga rakiyar kurayen da yake kira da sunan shugabanni. Ya dawo daga tumasancin da ya sanya kansa ga barayin dukiyarsa. Lallai ne ya kamata ya gane cewa shi ne dan kasa kuma mai hakki da dukiyar kasa.

Kamata ya yi ya gane cewa yana da ikon ya zabi wanda zai kula masa da dukiyarsa bisa gaskiya da amana. Kamata ya yi talaka ya gane cewa kansilan unguwarsa da shugaban karamar hukumarsa da gwamnan jiharsa da shugaban kasarsa da sauran dukkan ’yan majalisar da ke wakiltar yankinsa, dukkansu bayi ne a gare shi. Yana da ikon ya ce ya amince da su ko akasin haka. Don haka da zarar bai amince da yadda ake mulkinsa ba, zai iya cewa “na ki!”

Amma inda gizo ke sakar shi ne, yaya za a yi talaka ya gane martaba da mutuncin kansa? Lallai ne yana bukatar ingantacce, amintacce kuma kwararren jagora, wanda zai jagorance shi domin ya dauki irin wadannan matakai da na lissafa a baya. Allah Ya kawo wa talakan Najeriya sahihin jagora!

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin