✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rinjayen Jam’iyyar PDP a majalisar kasa na rawa

Sakamakon komwar gwamnoni biyar zuwa APC daga PDP, yanzu hankali ya koma Majalisar Dattawa da ta Wakilai don ganin yadda lamarin zai kaya.Jam’iyyar PDP tana…

Sakamakon komwar gwamnoni biyar zuwa APC daga PDP, yanzu hankali ya koma Majalisar Dattawa da ta Wakilai don ganin yadda lamarin zai kaya.
Jam’iyyar PDP tana da cikakken rinjaye a Majalisar Dattawa da sanatoci 74 daga cikin 109, sai dai wannan dama tana rawa sakamakon yadda ake jin sanatoci da dama za su bi gwamnonin biyar zuwa APC.
A Majalisar Wakilai a yanzu haka PDP tana da wakilai 208 ne yayin da APC ke da138, sai dai jihohi biyar da gwamnoninsu suka koma APC, wato Kano da Ribas da Adamawa da Kwara da Sakkwato suna da jimillar wakilai 48, kuma 40 daga cikinsu ana da yakinin suna tare da sabuwar PDP. Don haka idan suka koma APC, jam’iyyar za ta kasance tana da wakilai 178 inda za ta bar PDP da 168.
Wani dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano daga Jam’iyyar PDP Aliyu Sani Madaki ya ce wannan lokaci suke jira inda za su yi ban kwana da PDP. Ya ce babu dalilin da za su ci gaba da zama a PDP lura da irin musgunawar da ake yi wa shugabanninsu a ’yan watannin nan.
“Tabbas za mu i gwamnanmu Kwankwaso. Babu shakka kan haka. Dukkanmu ’yan PDP daga Kano za mu tafi baya ga wakilai biyu, Muhammad Bashir Galadanchi da Farouk Lawan, wadanda ba sa tare da mu,” inji shi.
Ya ce idan dukkansu da ke sabuwar PDP suka koma APC, hakan zai canja shugabancin majalisar domin APC za ta zamo mai rinjaye. “Ba za mu zauna a PDP mu ci gaba da ganin irin wannan zalunci ba. Ba za mu iya daukar wannan wulakanci da suke yi ga shugabanninmu ba. Idan dukkanmu muka sauya sheka na iya canja shugabancin majalisar,” inji shi. 

A kasa ga jadawalin sanatocin da ake jin za su koma APC, bayansu ana jin akwai sanatocin da za su iya bin su zuwa APC.
Jiha        Sanata
Adamawa                 2    Hassan Barata da Jibrilla Bindo
Kano                          1     Garba Lado
Ribas                          2                    Magnus Abe  da Wilson Asinobi
Sakkwato                  3    Ahmed Maccido da Umaru dahiru da Ibrahim Gobir
Kwara                         2     Bukola Saraki  da Shaba Lafiagi
Taraba                        1                  Jummai Alhassan
Gombe                       1      danjuma Goje
Nasarawa                  2     Abdullahi Adamu da Suleiman Adoke
Jam’iyyar LP tana da sanatoci uku – biyu daga Ondo daya daga Filato, yayin da Jam’iyyar APGA ke da sanata daya Chris Anyawu daga Imo.