✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rita, Olamide, Iyanya sun haskaka a gasar NEA

Fitacciyar jarumar fina-finan Kudanci Najeriya (Nollywood) da shahararrun mawaka, Olamide da Iyanya sun haskaka a yayin bikin Nigeria Entertainment Award (NEA) da aka gudanar a…

Rita Dominic rike da kyautartaFitacciyar jarumar fina-finan Kudanci Najeriya (Nollywood) da shahararrun mawaka, Olamide da Iyanya sun haskaka a yayin bikin Nigeria Entertainment Award (NEA) da aka gudanar a dakin taro na skirball Performing Centre da ke jami’ar New York a Amurka.
dan kama Basketmouth ne ya zama mai gabatar da taro, inda ya gayyato mawaki Mish da ’yan rawarsa daga Calabar, Jihar Kuros Riba.
Sauran mawakan da suka barje guminsu sun hada da Iyanya da Emma Nyra da Niyola da Phyno da Ajebutter 22 da Dammy Krane da kuma Sean Tizzle.
Jaruma Rita Dominic ce ta zama Gwarzuwar Jaruma, inda albam din YBNL na Olamide ya zama Gwarzon Albam, wakar Kukere ta Iyanya ta zama Gwarzuwa Waka.   Ice Prince ne Gwarzon Mawakin Gambara (Rap).
An kammala bikin da wakar Phyno da Olamide mai suna ‘Ghostmode”.
Ga jerin wadanda suka samu nasara a bikin:
Gwarzuwar Jaruma: Rita Dominic da fim din ‘The Meeting’. Mai tallafa wa Gwarzon Jarumi: Ali Nuhu (Blood And Henna). Gwarzon Jarumi: Tunde Aladese (Confusion Na Wa). Gwarzon Darakta: Tunde Kelani (Maami). Gwarzon Furodusa: Obi Emelonye (Last Flight to Abuja). Gwarzon DJ: DJ Bayo. Gwarzon dan Kama: Basketmouth. Gwarzon Albam: YBNL na Olamide. Gwarzuwar waka: Kukere ta Iyanya. Gwarzon Jarumi mai tasowa: Burna Boy. Gwarzon Pop/RnB: Dabido. Gwarzon Mawakin Gambara: Ice Prince.