✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldinho ya kashe Naira miliyan 9 a gyaran gantso

Shahararren dan kwallon Brazil da ya taba yin kwallo a kulob da dama ciki har da FC Barcelona na Sifen da kuma AC Milan da…

A hagu, Ronaldinho yana dariya bayan an yi masa aiki yayin da a dama a lokacin da yake da gantsoShahararren dan kwallon Brazil da ya taba yin kwallo a kulob da dama ciki har da FC Barcelona na Sifen da kuma AC Milan da ke Italiya Ronaldinho ya kashe zunzurutun Dala dubu 58 kwatankwacin Naira miliyan 9 da dubu 300 wajen gyara masa setin hakoransa da aka fi sani da gantso a Hausa.
Ronaldinho dai ya kasance mutum me mai gantso a baya inda hakoransa ke hargitse da hakan ta sa ba ya iya rufe baki a mafi yawan lokuta kamar mai yin murmushi.
dan kwallon mai kimanin shekara 33 ya ce ya dade yana tunanin zuwa asibiti don a gyara masa jerin hakoransa amma sai a wannan lokaci abin ya tabbata.
An gudanar da aiki ne a wani asibitin hakora da ke kasar Brazil a watan jiya amma  labarin bai bazu ba sai a ranar Litinin din nan da ta gabata bayan da dan kwallon ya tura bayanin haka a yanar sadarwarsa ta Twitter.
Ya zuwa wannan lokaci, hakoran dan kwallon sun koma daidai kamar na kowa, kamar yadda hotunan da ya aika yanar gizo suka tabbatar.
Ronaldinho, wanda yanzu haka yake buga kwallo a Brazil, ya shahara a lokacin da ya yi kwallo a kulob din FC Barcelona.  Hasalima ya taba lashe gwarzon dan kwallon duniya sau biyu a lokacin da yake kulob din Barcelona ta Sifen a shekarun baya.