✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya riga Messi zura kwallo ta 600 a raga

Shahararren dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo a ranar Lahadin da ta wuce ya samu nasarar zura kwallonsa ta 600. Ya samu nasarar kaiwa ga wannan…

Shahararren dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo a ranar Lahadin da ta wuce ya samu nasarar zura kwallonsa ta 600.

Ya samu nasarar kaiwa ga wannan matsayi ne bayan ya zura kwallo a ragar Inter Milan a gasar Rukunin Serie A, ta Italiya.  An tashi wasan ne ci 1-1 kuma Ronaldo ne ya zura kwallon inda ya taimaki kulob dinsa Jubentus aka tashi wasan kunnen doki.

Wannan matsayi da Ronaldo ya kai, ya zarce dan kwallon kulob din FC Barcelona na Sifen a wajen yawan zura kwallaye.  Kawo yanzu Messi  ma yana da yawan kwallaye 600 ne bayan ya zura kwallaye biyu a ragar Liberpool a shekaranjiya Laraba. Sai dai Ronaldo ya riga shi kaiwa ga wannan matsayi tun a ranar Asabar da ta wuce.

Ronaldo ya samu nasarar zura wadannan kwallaye ne a kulob da dama da suka hada da Sporting CP na Portugal da Manchester United da ke Ingila da Real Madrid da ke Sifen da kuma Jubentus na Italiya.

A bangaren Messi kuwa a kulob din FC Barcelona ne kadai ya yi wasa inda ya zura wadannan kwallaye.

Bincike ya nuna ba a hada kwallayen da Ronaldo ya zura a lokacin da ya yi wa Portugal wasa ba, kamar yadda ba a hada kwallayen da Messi ya zura a raga a yayin da yake yi wa Ajantina kwallo ba.