✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya sabunta kwantaraginsa a Real Madrid

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon kafa a a kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya sabunta kwantaraginsa…

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon kafa a a kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya sabunta kwantaraginsa da tsawon shekara uku da kulob din.  Hakan ta sa rade-radin da ake yi na barin dan kwallon kulob din ta zo karshe.
Yanzu kwantaratin dan kwallon zai kare ne a shekarar 2018 maimakon a 2015.
Haka kuma kulob din ya bayar da sanarwar kara wa dan kwallon albashi.
Da wannan kari, dan kwallon ya zarce kowane daukar albashi a daukacin Sifen ciki har da shahararren dan kwallon FC Barcelona Lionel Messi.
Kafin wannan lokaci, an rika rade-radin dan kwallon zai koma tsohon kulob dinsa watau Manchester United da ke Ingila amma yanzu an cimma matsaya a tsakaninsa da kulob din Madrid don haka maganar canza shekarsa ma ba ta taso ba.
Jaridar Marca da fitowa a Sifen ta kalato dan kwallon ya samu karin albashin Fam dubu 900 a duk shekara fiye da Lionel Messi.
Sannan jaridar ta kara da cewa, kulob din Madrid ya cimma matsaya a kan  yadda za su rika raba ribar tallace-tallace a tsakaninsa da Ronaldo.
 Kulob din Madrid ya sayo Ronaldo ne daga Manchester United da ke Ingila a shekarar 2009 a ciniki mafi tsada a duniya na Fam miliyan 80.
A halin yanzu Ronaldo shi ne na biyu a ’yan kwallon da suka fi karbar albashi mafi tsoka a duniya.
Samuel Eto ne na farko da albashin Yuro miliyan 20 a shekara. sai Ronaldo na biyu da Yuro miliyan 17 sai Lionel Messi na uku da Yuro miliyan 16 sai Neymar da Yuro miliyan 15 da sauransu.