✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya sayi mota mafi tsada a duniya

Rahoto ya nuna cewa shahararren dan kwallon  nan na kasar Fotugal da yake buga wa kulob din Jubentus na Italiya kwallo, Cristiano Ronaldo ya sayi…

Rahoto ya nuna cewa shahararren dan kwallon  nan na kasar Fotugal da yake buga wa kulob din Jubentus na Italiya kwallo, Cristiano Ronaldo ya sayi wata mota kirar Bugattu La Boiture Noire da ake ganin ita ce mota mafi tsada a duniya.

Ronaldo ya sayi motar ce a kan Fam miliyan 9 da dubu 500 (kimanin Naira biliyan 4 da miliyan 475 da dubu 500).

Rahoton da jaridar Marca ta Sifen ta kalato ya nuna cewa dan kwallon ya ba wani kamfani ne kwangilar kera masa motar wadda babu kamarta a duniya.

Kamfanin ya nuna wa duniya samfurin motar ce a wani bikin nuna motoci na bana da aka yi a Geneba  na kasar Suwizilan.

Kafin yanzu an dauka Shugaban Kamfanin Kera Motoci na Bolkswagen, Ferdinand Piech ne ya mallaki wannan mota, amma bayan kamfanin ya sanar da duniya ne aka tabbatar Ronaldo ne ya mallaki motar.

Sai dai rahoton ya ce Ronaldo ba zai fara amfani da motar ba sai a shekarar 2021 kamar yadda kamfanin ya fitar a wata sanarwa.  Kamfanin ya ce har yanzu bai kammala kera motar ba amma ana sa ran nan da 2021 dan kwallon zai fara amfani da ita.

Masayo kwallon kafa sun shaidi Ronaldo a matsayin dan gaye da hakan ya sa duk abin da yake amfani da su walau na sutura ko gida ko mota masu tsada ne.

Samuel Eto, dan kasar Kamaru ne ake ganin ya mallaki motar da ta fi tsada a tsakanin ’yan kwallon Afirka da ke wasa a Nahiyar Turai.  An kiyasta motarsa a kan Naira miliyan 300 sai dai sabuwar motar Ronaldo ta ninka tasa fiye da sau 15 a tsada.